Bankuna sun zama gurare mafi hatsari a Nijeriya, inji Birtaniya

*Ta gargaɗi ’yan ƙasarta da su guji zuwa bankuna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙasar Birtaniya ta sake fitar da wata sanarwar bada shawara ga ‘yan ƙasarta mazauna Nijeriya game da zuwa bankuna da ziyartar wasu jihoji a faɗin Nijeirya, na biyu a cikin watanni huɗu.

A cikin bayanin da aka sabunta ranar Laraba, Ofishin Harkokin Waje, FCDO, ya yi gargaɗi ga ’yan ƙasar Birtaniya a Nijieriya game da zuwa wuraren da akwai bankuna da ATM.

An yi nuni da cewa sake fasalin Naira da babban bankin Nijeriya ya yi tare da fitar da sabbin takardun kuɗi na N200, N500 da N1000 ya haifar da ƙarancin kuɗaɗe.

An samu ɓarkewar tashe-tashen hankula a wasu jihohin Kudancin ƙasar sakamakon ƙarancin kuɗi, tare da yin illa ga wasu garuruwa a faɗin aasar.

“Muna ba da shawara ga ’yan ƙasarmu a Nijeriya da su yi amfani da hankali, gami da sanin duk wani babban taron jama’a ko kuma inda wata matsala ta ke,” in ji FCDO.

Birtaniya ta bayyana cewa, da ƙaruwar ayyukan aikata laifuka, tana ba da shawarar ga ‘yan ƙasarta da su yi taka tsantsan musamman lokacin fitar da kuɗaɗe a wuraren cunkoson jama’a, da kuma cikin lokutan dare.

An kuma gargaɗi su kan tafiye-tafiye zuwa jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Kaduna, Katsina, Zamfara, Dalta, Bayelsa, Ribas da Akwa Ibom.

FCDO tana ba da shawara kan duk wani balaguron zuwa Bauchi, Kano, Jigawa, Neja, Sakkwato Kogi, Kebbi, Abiya, Filato da Taraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *