Farashin kaya ya tashi saboda ƙarancin Naira na cigaba da tsananta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya sake tashi zuwa matsayi mafi girma da kashi 21.82 a watan Janairu daga kashi 21.34 cikin ɗari a watan Disambar bara.

Wannan na zuwa ne a rahoton baya-bayan nan da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar ranar Laraba, 15 ga Fabrairu, 2023.

Sabon ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ya zo ne a daidai lokacin da ’yan Nijeriya ke fuskantar rashin matsalolin tattalin arziki sakamakon ƙarancin kuɗin da aka yi wa kwaskwarima na Naira.

Wannan ƙaruwar na Janairu yana nuna ƙaruwar kashi 0.47 idan aka kwatanta da 21.34 da aka rubuta a cikin watan da ya gabata.

Hauhawar farashin kayan abinci ya haura zuwa kashi 24.32 a cikin Janairu daga 23.75 da aka rubuta a watan Disamba 2022, yayin da ainihin hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya keɓance farashin kayan amfanin gona ya tsaya a kashi 19.16 a cikin watan bara idan aka kwatanta da kashi 18.49.

Musamman, an sami ƙaruwa mafi girma a farashin gas, man fetur, jigilar fasinja ta jirgin sama, kayan aikin motoci, kayan sufuri da sauransu.

A halin da ake ciki kuma, ta fuskar ƙididdigar abinci, an danganta hauhawar farashin kayayyakin abinci da ƙarin farashin wasu kayayyakin abinci kamar su burodi da hatsi, kifi, dankali, dawa, doya da dai sauransu.