Taron tunawa da marubuci Mahmoon Baba-Ahmed ya yi armashi

Daga AISHA ASAS

Kamar yadda Manhaja ta shelanta a makon da ya gabata cewa, shahararriyar ƙungiyar nan ta marubata da ke Jihar Kaduna, wato Ƙungiyar Marubuta Alƙalam ta shirya tsaf don gudanar da taro na musamman don tunawa da fitacce kuma shahararren ɗan jarida kuma marubuci, marigayi Mahmoon Baba-Ahmed, wanda ya kasance jagaba kuma ginshiqi na cigaban da ƙungiyar ta samu.

Ƙungiyar mai ɗauke da manyan marubutan da Jihar Kaduna ke alfarahi da su, ta sanar da ƙaddamar da litatafin marigayin na ƙarshe, wanda ya rubuta, amma bai samu damar bugawa kafin Allah Ya ɗauki ransa ba, duk dai a ranar ta Alhamis, 9 ga Fabrairu, 2023.

An fara gudanar da taron ne da misalin ƙarfe 11:44 a ɗakin taro na Gidan Arewa da ke cikin garin Kaduna, yayin da aka soma da buɗe taro da addu’a daga bakin Alhaji Balarabe Idris Jigo. Shugaban taro Ciyaman na Liberty, Dakta Ahmed Tijjani Ramalan, a ƙarƙashin wakilcin Alhaji Muhammad Iskil Abdullahi ne ya gabatar da jawabin buɗe taro.

Shugaban kwamitin shirya taron, Malam Ibrahim Sheme tare da biyu daga cikin ‘ya’yan kungiyar, Khadija Abdullahi Mahuta da Fatima Abba Gana

A jawabin nasa, ya bayyana marigayi Mahmoon a matsayin mutumin da ya sha gwagwarmaya wurin ƙoƙarin kawo sauyi ga cigaban qasa bakiɗaya. Ya kuma bayyana shi a matsayin mutum mai amana tare da aiki tuƙuru.

Shugabar ƙungiyar, marubuciyar ‘Sanadin Boko’ da kuma ‘Fuska Biyu’ Halima Abdullahi K/Mashi ita ma ta yi nata jawabin na maraba, sannan kuma ta bayar da tarihin kafuwar ƙungiyar da yadda marigayin ya tallafi ƙungiyar zuwa matakin da ta ke kai a yanzu.

Daga ƙarshe ta bayyana ƙungiyar a matsayin wani abu da Baba-Ahmed ya bari da za a dinga tunawa da shi. Kuma ta yi godiya ga waɗanda suka taimaka har taron ya kasance da kuma mahalarta taron bakiɗaya.

Daga cikin waɗanda suka yi jawabi a taron akwai Daraktan Shiyyar Kaduna na Hukumar Gidajen Rediyo Tarayyar Nijeriya (FRCN), Alhaji Buhari Auwalu, wanda ya bayyana wa mahalarta taron wuraren da Mahmoon Baba-Ahmed ya yi aiki da kuma muƙaman da ya riƙe a aikin jarida.

Ya ce, ya yi wakilci gidajen rediyo da dama a wasu jihohi, musamman Kano, inda ya yi fice. Kuma ya riƙe muƙamin shugaban gidan Rediyon Jihar Kano, daga baya kuma ya zama shugaban Hukumar Yaɗa Labarai ta Jihar Kaduna (KSMC).

A jawabin nasa, ya ce, marigayin bai huta ba ko ya zubar da aikin jarida a lokacin da ya yi ritaya ba, asali ma ya sake riƙe wasu muƙamai ne a wasu kafafe kamar DITV da Liberty. A wani ɓangare ya kafa jarida sukutum tasa mai suna Sawaba, sannan ya rubuta littafai har guda shida. Duk waɗanan sun faru ne bayan ya yi ritaya.

Iyalan Malama Fatima Yusuf Muhammad yayin karbar lambar yabon

Daga ƙarshe ya kira marigayi Baba-Ahmed da ɗan jarida mai faxar gaskiya komai ɗacin ta, ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan sa da rahma.

Farfesa Adamu Ibrahim Malumfashi na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya ne ya yi sharhi kan littafan marigayi Baba-Ahmed guda shida, wato ”Yar Halas’, ‘Uwani Reza’, ‘Ɗan Hausa’, da littattafai uku na mashahurin marubucin nan William Shakespeare da ya fassara su zuwa harshen Hausa, wato Macbeth (‘Makau’), Julius Caesar (Jarmai Ziza’), da Romeo and Juliet ‘Habiba Ta Habibu’ wanda shi ne aka ƙaddamar a ranar taron.

Daga ƙarshe ya bayyana marigayi Mahmoon Baba-Ahmed a matsayin babban marubuci da ya yi aikin da ya cancanci jinjina, ya kuma cancanci a kira shi a layin manyan marubutan da Arewa da ƙasa bakiɗaya ke alfahari da su.

Shi ma Dakta Yusuf Nadabo, Sarkin Tudun Nufawa, Kaduna, wanda babban malami ne a Jami’ar Zariya ya yi nasa jawabin, domin shi ne ya gabatar da littafin Mahmoon na ƙarshe, wanda ake ƙaddamarwa, wato ‘Habiba Ta Habibu’.

A ɓangaren marubuta kuwa, fitaccen marubucin nan kuma shugaban ƙungiyar masu shirya finafinai ta Jihar Kano, wato MOPPAN, Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, shi ma ba a bar shi a baya ba, domin ya yi jawabi kan ayyukan da marigayi Baba-Ahmed ya gabatar kafin rasuwarsa tare kuma da saka muryar wasu daga cikin ayyukan da ya yi da kuma nuna hotunansa a wasu lokuta baya.

Sha’iri Malam Garba Lawal Buruku da kuma Malam Nafi’u ne suka gabatar da waƙoƙin ta’aziyyar marigayin, kafin faifan waƙar Malam Yahaya Makaho ga ƙungiyar ya karaɗe ɗakin taron.

A ɓangaren makusantar marigayin su ma sun sanya albarka a taron, domin aminin marigayin Malam Abdullahi Nuhu, mai ɗakin marigayin Hajiya Mama Zainab da kuma babban ɗansa Aminu Mahmoon duk sun tofa albarkacin bakinsu. Cike da alhini suka yi addu’ar rahma ga mamacin tare kuma da godiya ga mahalarta.

Daga nan ne taron ya shiga rukunin qarshe na jadawalin gudanarwa, inda aka bayar da lambar girmamawa ga marigayin. Ɗansa Malam Aminu Mahmoon ne ya karɓa. Ba shi kaɗai ba, ƙungiyar ta bayar da lambar ga wasu ‘ya’yan qungiyar har biyu da suka rigamu gidan gaskiya. Hajiya Amina Haske, wadda ta kasance marubuciya da ta jima tana bada gudunmuwa ga cigaban adabin kasuwar Kano da kuma Hajiya Fatima Yusuf Muhammad, mataimakiyar shugabar wannan ƙungiya ta Alƙalam, kuma jajirtacciyar marubuciya da ta jima a ƙungiyar tana bada tallafin nata ilimi wurin ganin ƙungiyar ta kai mataki na ban sha’awa.


Su ma dai iyalansu ne suka karɓi wannan lambar girmamawa cike da alhini, domin har zubar da ƙwalla wasu daga cikin su suka yi don tunawa da irin rashin da suka yi.

Iyalan Amina Haske

Jawabin shugaban kwamitin shirya taron, Malam Ibrahim Sheme ne ya zama na ƙarshe, inda ya yi godiya ga ilahirin waɗanda suka samu damar halartar taron. Daga nan taro ya tashi da misalin ƙarfe 3:35.

Tabbas taron ya amsa sunansa na taro, kuma Ƙungiyar Marubuta Alƙalam ta nuna tabbacin halaccin ta ga marigayi Mahmoon Baba-Ahmed tare da tabbatarwa da duniya cewa, ba za ta tava mantawa da namijin ƙoƙari da marigayin ya yi wa ƙungiyar ba.

Bayan kasancewar Mahmoon Baba-Ahmed fitaccen ɗan jarida kuma ƙwararren marubuci, mutumin kirki ne da ke shimfiɗa fika-fikan rahma ga duk wanda ya zo neman taimakon sa, musamman ma marubuta, domin ya ɗora marubuta da dama kan hanyar da a yau suke cin moriyar ta, don haka zai jima bai gushe daga tunanin ɗinbin mutanen da ya haska rayuwarsu ba.

Allah ya jiƙan marubuci kuma ɗan jarida Alhaji Mahmoon Baba-Ahmed.