Masu sayar da Naira za su fuskanci ɗauri a gidan yari – CBN

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da ake tsaka da halin matsi a sakamakon canjin kuɗin Nijeriya, Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya sha alwashin cafkewa da gurfanar da duk wani mai POS ko makamancinsa da aka samu da sayar da takardun Naira a matsayin kuɗin hada-hada (cajis). CBN ya ja kunne cewa, wannan lafi ne da yake da alaƙa da rashawa kuma laifi ne da zai iya sa a kulle mutum a gidan kaso.

A cewar babban bankin, an yarda da biyan kuɗin ladan hada-hada wanda ake cewa cajis. Kuma a cewar sa, ba a haramta wannan ba. Amma wannan cajin na rashin hankali da ya wuce ƙa’ida shi ne laifi a hukumance. Misali kamar a ba da Naira dubu 5 a kan Naira dubu 7 ko dubu 10 a kan Naira dubu goma sha biyu da sauransu.

Wannan gargaɗi yana zuwa ne bayan CBN ya nuna damuwarsa a kan duk da yawan kuɗaɗen da babban bankin ya saki, ba a dawo da kuɗaɗen cikin banki. Wanda a cewar sa hakan abin mamaki ne.

A yayin da yake hira da ‘yan jaridu a reshen CBN na Yenagoa Daraktan ofishin gwamnan CBN, Mista Joseph Omayuku, ya bayyana cewa, a yanzu haka jamian tsaro sun baza komarsu don kamawa da gurfanar da duk wani mai POS da wakilan kuɗi da suke damfarar ‘yan Nijeriya a matsayin cajin hada-hadar kuɗi.

Omayuku ya ƙara da cewa, hukunci mai tsanani yana nan yana jiran bankuna ko ma’aikatan bankuna a kan wannan ɗabi’a ta rashin gaskiya. Kuma duk wanda aka tabbatar da yana yi wa tsarin CBN ɗin zagon ƙasa, za a hukunta shi.

Sannna ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ƙara haƙuri domin bankin yana nan yana iya ƙoƙarinsa don ganin komai ya daidaita.

Sanan kuma a cewar sa, manufar canza kuɗin nan shi ne kuɗi su cigaba da zagawa tsakanin al’umma da bankuna. Amma abin mamaki sababbin kuɗaɗen ba sa dawowa cikin bankin.