Benzema ya kafa tarihin yawan cin ƙwallaye a La Liga

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Karim Benzema ya kafa tarhin zama na biyu a yawan cin ƙwallaye a gasar La Liga a Real Madrid.

Ranar Laraba, Real ta doke Elche 4-0 a wasan mako na 21 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu.

Marco Asensio ne ya fara cin awallo, sai Karim Benzema ya zura biyu a raga duk a bugun fenariti, sanan Luka Modric ya ƙara na huɗu

Benzema ya ci ƙwallo 230 kenan, shine na biyu a yawan ci wa Real Madrid ƙwallaye a La Liga, ya haura Raul mai riƙe da gurbin.

Cristiano Ronaldo kyaftin tawagar Portugal shi ne kan gaba a yawan ci wa Real Madrid ƙwallaye a babbar gasar tamaula ta Sifaniya mai 311.

Yayin da Barcelona za ta kara da Manchester United ranar Alhamis a Europa League, Real ta rage tazarar maki 11 da ke tsakaninta da Barcelona ta ɗaya ya koma takwas.

Real ta buga wasa da Elche ranar Laraba ne, bayan da ta je Morocco ta lashe FIFA World Club Cup.