Daga MOH BELLO a Zariya
Limamin masallacin Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi dake Ƙofar Gayan Low-cost cikin Ƙaramar Hukumar Zariyan Jihar Kaduna, Sheikh Muhammad Aliyu ya gargaɗi Musulmi da su guji danganta kansu da sharholiyar ranar masoya wanda ake yi 14 ga Fabrairun kowace shekara.
Ya yi wannan gargaɗin ne a cikin hudubarsa ta ranar Juma’ar makon da ya gabata, inda malamin ya ce wannan sharholiyar (valentine) ya saɓa wa koyarwar addinin Musulunci, “don haka ahir ɗin dukkan Musulmi.”
Sheikh Muhammad Aliyu ya ce dukkan yin wannan ta ranar masoya waɗanda suka jiɓanci sheɗan ne.
“Bikin sharholiyar (valentine day) fasiƙanci ne, ya kamata duk su ƙyamace shi saboda ba komai ciki sai halaka,”inji malamin.
Da ya juya kan batun canjin kuɗi, Sheikh Aliyu ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta dubi halin ƙunci da jama’ar ƙasa musamman talakawa ke ci.
Limamin ya ƙara da cewa al’umma na fama da yunwa sakamakon wannan wa’adin canji sakamakon rashin sabbin kuɗi, su kuma tsoffin ba a karɓan a mu’amalolin kuɗin na yau da kulum.
Ya kuma buƙaci gwamnatin ta fito da wani don aiwatar da wannan canjin kuɗi ta hanyar da talakawa ba za su tagayyara ba.
