Zaɓen 2023: FRSC za ta bada goyon baya don samun nasara: Kwamanda Auwalu Mohammed

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Kwamandan Hukumar Kula da Manyan Hanyoyi da Kiyaye Haɗura ta Ƙasa, (FRSC), reshen Ƙaramar Hukumar Keffi a Jihar Nasarawa, Auwalu Magaji Mohammed, ya ce a shirye hukumar take shiyyar ta bada nata gagarumar gudunmawa don tabbatar da nasarar zavukan gama-gari na shekarar 2023 dake tafe a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Kwamanda Auwalu Magaji Mohammed ya bayyana haka ne a
lokacin da yake tattaunawa da wakilin Blueprint Manhaja a ofishinsa dake garin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a jihar ranar Laraba 15 ga Fabrairun shekarar 2023 da ake ciki.

Ya ce ba shakka kamar sauran hukumomin tsaro daban-daban a jihar, hukumar FRSC a shiyyar ita ma tana da haƙƙin yin duka mai yuwa wajen tabbatar da an gudanar da zaɓukan cikin tsari ba tare da an fuskanci matsaloli ba, musamman a fannin kare haɗuran ababen hawa.

Ya ce ayyuka da hukumar za ta gudanar a lokaci da kuma bayan zaɓukan sun haɗa da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro a yankin da jihar baki ɗaya wajen samar da tsaro a runfunan zaɓen da kula da masu ababen hawa don tabbatar suna bin dokokin tuƙi a hanyoyin jihar a lokacin kamar yadda take yi a yanzu da sauransu.

Kwamandan ya kuma yi amfani da damar, inda ya sanar cewa tuni a yanzu hukumar a shiyyar ta ƙaramar hukumar Keffi a ƙarƙashin jagorancinsa ta fara horar da jami’anta akan dabarun aiki na musamman kafin lokaci da kuma bayan zaɓukan.

Ya ƙara da cewa har ila yau hukumar takan gana akai-akai da takwarorinta sauran hukumomin tsaro a duka matakai a jihar, inda suke tattauna yadda za su yi aiki tare wajen tabbatar da nasarar zaɓukan a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Daga nan sai Kwamanda Auwalu Magaji Mohammed ya kuma yi amfani da damar, inda ya yi kira na musamman zuwa ga al’ummar yankin ƙaramar hukumar Keffi da kewayenta da jihar baki ɗaya su guji karya dokokin hukumar musamman waɗanda suka shafi zaɓukan na 2023 don a cewarsa duk wanda hukumar ta kama da laifin za ta hukunta shi daidai da laifin da ya aikata.