Sarkin Kano ya yi kira kan zaɓen shugaba nagari

Spread the love

Daga RABIU a SANUSI Kano

Mai Martaba Sarkin Kano, Dr. Aminu Ado Bayero, ya bukaci al’umma da su zaɓi cancanta a wannan zaɓen.

Dr. Aminu Ado Bayero ya yi wannan kira ne jim kaɗan bayan ya dangwala ƙuri’arsa a akwatinsa da ke cikin Ado Bayero Islamiyya a fadar sa, birnin Kano.

Sarkin ya ce kamar yadda kowa ya sani yau ce ranar da ake zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya.

“Kamar yadda kowa ya fito yake zaɓe mu ma yau ya dace mu fito mu gudanar da namu zaɓen ga wanda muka san ya cancanta da muke ganin zai iya kawo mana cigaba a ƙasar nan.”

Mai martaba ya yi addu’ar kada Allah Ya bar mu da zaɓin mu, Ya zaba mana abin da ya fi alkhairi a wannan zaɓe.

Daga karshe ya yaba da yadda zaɓen ke gudana cikin kwanciyar hankali da lumana.

By Editor