Ana zargin Barcelona da bai wa alƙalan wasa cin hanci

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ana zargin Barcelona ta biyan alƙalan wasa Yuro miliyan 8.4 don a riqa yi mata alfarma a wasanni

’Yan sandan Sifaniya sun kai samame hedikwatar alƙalan wasan ƙasar a wani ɓangare na binciken zargin cin hanci da ake yi wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona.

Barcelona na fuskantar zargin cin hanci kan wasu kuɗaɗe da ta tura wa Jose Maria Enriquez Negreira, wani tsohon mataimakin shugaban kwamitin alƙalan wasan, don a riƙa yi musu alfarma a wasanninsu.

Barcelona ta musanta zargin kuma ba a kama kowa ba a lokacin samamen a birnin Madrid.

Ba a kai takardun ba kuma dalilin da ya sa aka ɗauki matakin kai samamen ke nan a ranar Alhamis.

Tun farko, ofishin shigar da ƙara na Barcelona ne ya tayar da batun a watan Maris, inda ita ma hukumar ƙwallon Turai ta ƙaddamar nata binciken jim kaɗan bayan haka.

By Editor