’Yancin ’yan jarida a gwamnatin Tinubu

Spread the love

Duk da dai an samu wata ’yar taƙaddama a tsakanin sabuwar gwamnatin Alhaji Asiwaju Chif Bola Ahmed Tinubu a gefe guda yadda tun a karon farko a ka zaɓo fitacce kuma zaƙaƙuri ta fuskar masaniya da aikin kafafen yada labarai. Kuma a kai mai muƙami na minista.

Alh Idris Muhammed Malagi zamowar sa minista a ɓangare na labarai da wayar da kan al’umma hakan wata gata ce ga aikin jarida a dukkanin Arewa da ma dukkanin ƙasar mu Nijeriya.

Sai dai duk da haka a kula ita gwamnati uwa ga ’yan kasa ta yadda idan mutum ya bi doka ya zauna da i ta lafiya idan kuma an keta doka a samu matsala a tau yar shawara ga dukkanin ma su aiki na jaridu a kula. aikin jarida muhimmi ne domin wakilci ne a tsakanin talakkawa zuwa ga ma su mulki wanda hakan kadai ya isa mu ƙara jinjina a gare ku da fatan ku ƙara kwazo da kwatamta adalci a ayukkan ku. Allah ya iya ma ku ayyukan ku.

Kan batun umurnin shigo da shinkafar waje:

Alhamdulillahi, ga alamu gwamnatin Tinubu ta yi dogon nazari kuma mai amfani. Bayar da umurnin shigo da shinkafa ’yar waje hakan tamkar buɗe ƙofar sama ma talakkawa sauƙi ne daga wancen matsi na rayuwa wanda ya samu asali daga gwamnatin baya.

duk da cewa a nasu ɓangaren ma su aikin sarrafa shinkafa ’yar gida sun nuna damuwar su dangane da buɗe ma shinkafar waje qofa mu dai talakkawa hakan na a matsayin nema ma mu sauqi domin a kullum idan tsanani ya wanzu a kan talakka ya ke karewa.

Mu na fatan wannan gwamnati ta su Tinubu ta ƙara duba wasu hanyoyi na sauƙaƙa ma talakkawa tunda ga alamu ku na da tausayi da sauraren ƙorafin talakkawan ku. Ku kuma waɗanda ke sana’a ta sarrafa shinkafa ku dubi wahalar rayuwa da talakkawa ke ciki ba samayyar ku ba domin mu da ku duka bayin Allah ne. Ya Allah ka kawo mana sauƙi a rayuwa.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina, 07066434519/08080140820.

By Editor