NDLEA ta kama ton 15.7 na haramtattun ƙwayoyi a Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar NDLEA reshen jihar Kano a ranar Litini ta ƙona tan 15.7 na haramtattun ƙwayoyi da ta kama a jihar.

Shugaban hukumar Buba Marwa ya ce dakarun hukumar da jami’an tsaron tashar jiragen saman Malam Aminu Kano MAKIA suka kama haramtattun ƙwayoyin tsakanin watan Oktoba 2020 zuwa Oktoba 2023.

Marwa wanda Shugaban fannin gudanar da bincike na hukumar Samuel Bashir-Gadzama ya wakilta ya ce hukumar ta ƙona waɗannan muggan ƙwayoyi domin daƙile yaɗuwarsu cikin al’umma.

Shugaban hukumar na jihar Kano Abubakar Idris-Ahmad ya ce daga cikin tan 15,193.365 da aka ƙona akwai kilogiram 9,824.098 na ganyen wiwi, hodar ibilis 1.8665 kg, wasu qwayoyi masu nauyin 4,694.298 kg, Methamphetamine gram 9, Barbiturate 10 kg da 663 kg na magungunan da wa’adin amfaninsu suka ƙare.

Idris-Ahmad ya yaba ƙoƙarin gwamnatin jihar, alƙalai da jami’an tsaro da ƙungiyoyi masu zaman kansu kan yaƙi da suke yi domin hana safara da ta’ammali da muggan ƙwayoyi.

“Muna kuma miqa godiyarmu ga masarautun jihar kan mara wa gwamnati baya da su ke yi.”

Hukumar ta ce za ta buɗe ofisoshinta a duk ƙananan hukumomin ƙasar nan domin ƙarfafa yaƙi da muggan ƙwayoyi a ƙasar.

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnati Shehu Wada-Sagagi wanda ya wakilci gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati a shirye take domin kawar da waɗannan matsala daga jihar.

By Editor