Bambancin marubutan onlayin da mawallafa littattafai a bayyane yake – Milhart

“Ban yi wa marubuta adalci ba, idan na ce suna da girman kai”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Fadeela Yakubu matashiyar marubuciyar onlayin ce daga Jihar Gombe, wacce za a iya kiranta da ƴar baiwa, saboda yadda take da basira da hikimar yin abubuwa da dama a fagen ƙirƙira, domin ilimantar da matasa, faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa. Bayan kasancewarta marubuciya, Fadeela, wacce ake kira da Milhart, sananniya ce a manhajar Tiktok da YouTube, inda take wallafa kalaman soyayya da faɗakarwa, da kuma karanta littattafan Hausa. Allah Ya yi mata baiwa ta zaƙin murya ta yadda take amfani wannan baiwar da Allah Ya yi mata wajen isar da saƙonni ga masu bibiyarta ta hanyar waƙe-waƙe da kalaman hikima, bayan rubuce-rubuce da take yi a zaurukan sada zumunta. Wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya samu zantawa da wannan ƴar baiwa da ta bayyana irin ƙalubalen da ta fuskanta kafin ta kai ga matakin samun ɗaukaka a rayuwarta.

MANHAJA: Mu fara da jin sunan malamar.


MILHART: To, masha Allah. Da farko dai cikakken sunana shi ne Fadeela Yakubu wacce aka fi sani da Milhart. Ni marubuciya ce, mawaƙiya, kuma mawallafiyar kalaman soyayya da faɗakarwa a manhajar Tiktok. Kuma ina karanta littattafan Hausa a YouTube. Sannan har wa yau ni ma’aikaciyar lafiya ce, kuma ɗaliba mai neman ƙwarewa a fannin haɗa magunguna.

Za mu so jin taƙaitaccen tarihinki, wacce ce Fadeela?

Ni asalina haifaffiyar Jihar Gombe ce, daga Qaramar Hukumar Yamaltu-Deba. Na yi karatuna tun daga matakin firamare da sakandire a Ƙaramar Hukumar Biu da ke Jihar Borno, inda mahaifina ke aiki. Amma daga baya na koma Jihar Gombe, hakan ya bani damar cigaba da karatuna a wata makarantar koyar da aikin jinya da ke Gombe. Na kuma samu shaidar kammala diploma a fannin magunguna wato Pharmacy. Alhamdulillah.

Ko za ki faɗa mana yadda ki ka tsinci kanki a harkar rubuce-rubuce?

Tun tasowata na kasance mai yawan son karance-karance tun ina makarantar sakandire, amma sai bayan da na gama ne na fara sha’awar ni ma in rubuta nawa littafin. Kamar da wasa na fara rubuta wani littafina mai suna ‘Matar Aurena’ a shekarar 2018. A lokacin da na fara rubutun na tura wa wasu ƙawayena ta kafar sada zumunta a WhatsApp, don su karanta su bani shawara. Daga nan suka yaba sosai, suka yi ta cewa na cigaba, a cikin su akwai wata ƙawata Ummu Kulsum Musa wacce tafi kowa matsawa a kan na yi rubutun. Wata rana sai ta ce da ni me zai hana na shiga ƙungiyar marubuta inda zan samu masu taimaka min yadda zan rubuta nawa littafin. Haka kuwa sai na amince har ta haɗa ni da wani bawan Allah mai suna Hassan ATK wanda bayan mun yi magana da shi ya haɗa ni da shugabar ƙungiyar Manazarta Writers Association Binta Umar Abbale. Daga nan dai na zama cikakkiyar ƴar qƙungiyar bisa taimakonta, ta kuma riƙa koya min dabarun yadda zan inganta rubutuna, har dai na fitar da littafina na farko.

Ko za ki iya faɗa mana adadin littattafan da ki ka rubuta zuwa yanzu?

E, Alhamdulillahi. Na rubuta littafai 7, kuma yanzu haka ina cikin na 8 da izinin Allah. Daga ciki akwai, ‘Matar Aurena’, ‘Rayuwar Husna’, ‘Daliyah da Daniyah’, ‘Saira da Sarah’, ‘Matar Uba’, ‘Dangin Ubana’, ‘Jinnul Kamil’, ‘Haƙƙin So’, sai kuma ‘Mawaƙi’, da wani littafin haɗaka da muke yi mai suna ‘Wasa Da Rai’.

Ko za mu san wani abu a taƙaice game da littattafan da ki ka rubuta?

To, da farko dai shi littafin ‘Matar Uba’ labari ne kan wata yarinya da matar babanta take wahalarwa, har ta makantar da ita bayan ta kashe mahaifanta da ƙannenta. Shi kuma littafin ‘Rayuwar Husna’ labarin yaya da kanwa wanda kishi ya rufe idanun ƙanwar ta nemi hallaki ƴar’uwarta saboda son zuciya.

Littafin ‘Sairah Da Sarah’ da littafin ‘Daliya Da Daniya’ tagwayen littattafai ne da suke ɗauke da labarin wasu yaran mata ƴan biyu masu abin al’ajabi wanda komai a tare suke yi, idan ɗaya na kuka ko da basa tare sai ɗayar ma ta tsinci kanta tana kuka. Bayan rasuwar Sarah Daliya ta musulunta, sannan Sairah ta riƙe Daliya da Daniya.

Littafin ‘Dangin Ubana’ shi kuma labarin wani saurayi ne mai suna Haisam, wanda qanin mahaifinsa ya kashe masa uba, ya kuma yi sanadiyyar faɗawarsa cikin wata rayuwa mai ban tausayi.

Akwai kuma littafin ‘Jinnul Kamil’ wanda rubuta kan wata yarinya da ta yi sakaci kamilin aljani da ba a gane shi ya shiga jikinta, ya kuma rikita mata rayuwa. Shi kuma labarin ‘Mawaƙi’ da nake kan aiki yanzu labari ne na wani matashin mawaqi da yake fuskantar ƙalubalen rayuwa, a ƙoƙarinsa na samun ɗaukaka da farinciki a rayuwarsa.

Shin kin tava buga littafi ko a iya a onlayin ki ke wallafawa?

A’a, ban tava bugawa ba. Ni dai a iya onlayin nake fitarwa, amma ina da niyyar bugawa nan gaba, in sha Allah.

Ba mu labarin yadda aka yi ki ka samu kanki a harkar waƙa?

E, haka ne, ina tava yin waƙa duk da yake dai har yanzu ni ƴar koyo ce. Yadda aka yi na fara waƙa kuwa shi ne akwai wani mai suna Musa Yakubu Malam ana yi masa laqabi da Mr Em-Y. Mawaƙi ne ɗan Jihar Gombe. Muna da kyakkyawar alaƙa a tsakinin mu, wanda ya zamana ya zama tamkar yayana. A duk lokacin da muka yi waya yana yawan faɗa min cewa, muryarki za ta yi daɗi da waƙa.

Watarana kuwa ya gayyace ni inda suke ɗaukar waƙoƙi wato situdiyo ɗin sa, kamar da wasa ya kunna min wata waƙar aure da ya yi, sai ya ce min yana buƙatar a masa amshi. Sai ya faɗa min abinda yake so in faɗa da kuma salon da yake so, kamar da wasa na gwada kuma sai ya yi daɗi. Tun daga wannan lokacin duk yayin da yake buƙatar ƴar amshi zai kirani na yi masa. Bayan wani lokaci kuma sai wani abokinsa mai suna Saifullahi Ibrahim Shariff da ake ce wa Saiflex ya rubuta wata waƙa mai taken Uzuri ya bukaci mu yi tare, daga baya muka yi waƙar mu uku. Alhamdulillah waƙar ita ma ta yi daɗi ta kuma samu karvuwa fiye da yadda ba mu yi zato ba, saboda mun yi ne kawai don nishaɗi to, ka ji yadda aka yi na tsinci kaina a harkar waƙa.

Kina daga cikin matasan da ke tashe a manhajar Tiktok, inda ki ke wallafa kalaman soyayya da na faɗakarwa, yaya abin yake ne?

E, ina wallafa kalaman soyayya da ma zancen hikima har da na addini a zaurukan sada zumunta ba a Tiktok kawai ba. Kuma ina yin hakan ne don ganin na isar da saƙo da muryata, kuma alhamdulillahi ina samun karvuwa sosai. Na buɗe zaurena a manhajar Tiktok mai suna Milhart, kuma kamar da wasa a cikin wata ɗaya na samu masu bibiyata har mutum duba 87 da ɗari 7, amma cikin rashin sa’a aka rufe min zauren, saboda wasu dalilan da har yau ban san mai ya jawo aka rufe min ba. Sai dai na ji haushi matuƙa kuma na ji gwiwata ta yi sanyi, amma duk da haka ban karaya ba. Na sake buɗe wani sabon zauren Milhart, wanda a yanzu nake da mabiya dubu 23 da ɗari 8.

An ce kina karanta littattafan Hausa a YouTube, shin littattafanki ne ki ke ɗorawa ko na wasu marubutan ne daban, shin yaya ki ka samu kanki a wannan fagen shi kuma? Kuna samun amincewar marubutan kafin ku karanta?

Ina karanta littattafaina har ma da na wasu marubutan. Shi ma dai kamar da wasa wani mai amfani da manhajar YouTube mai suna Muhammad Kareem ya ce da ni, “ƙanwata, na buɗe Channel. Ina so mu yi aiki tare ki riqa karanta mana, ni kuma ina ɗorawa. In sha Allahu za mu samu alheri a ciki.” Da farko na qi yarda saboda ban taɓa yi ba, kawai dai nakan ji ana yi, amma a haka ya yi ta ƙarfafa min gwiwa akan zan iya, a hankali kuma na fara. Tun ina yi ba na jin daɗinsa har ya zame min jiki, wanda a dalilinsa yanzu haka ina yi wa masu amfani da YouTube da yawa aiki. Ni kaina ban san adadin su ba. Sai dai yawanci su ne suke sayen littafin daga marubutan, ko su daidaita a tsakaninsu, kafin su turo min ni kuma in karanta.

Shin kina ganin tsakanin hikimarki ta rubutu da fasaharki ta sarrafa murya wanne ya fi kawo miki ɗaukaka?

A gaskiya zan iya cewa, muryata ce sirrin samun ɗaukakata. Ina jin daɗi da godiya ga Allah da ya albarkace ni da murya mai daɗin amo da jan hankali, wanda jama’a da dama ke yabawa da ita. A cikin ƙanƙanin lokaci muryata ta shiga wurare da dama, musamman kalamaina na Tiktok ba a iya nan Nijeriya suka tsaya ba har makwaftanmu inda akwai Hausawa, kamar su, Ghana, Nijar, Libiya har ma da Saudiyya. Alhamdulillahi, a yanzu na kai matakin da idan wani ya nuna ya sanni ma sai a nemi ƙaryata shi. An sha kirana ana faɗa min na ji muryarki a wuri kaza amma an ƙaryatani, shi ne na kira ki. Idan suka ji muryata su yi ta mamaki! Ina samun kira da saƙonni da kuma addu’o’i daga masoya daban-daban, ina kuma jin daɗin hakan sosai.

Wanne ƙarfafa gwiwa za ki yi wa matasa masu baiwa irin taki kan amfani da zaurukan sada zumunta don cin moriyar basirarsu?

Kar ku karaya. Za ku iya. Ku jure, kuma ku yi haquri, sabida rayuwa cike take da ƙalubale. Idan ku ka duba kamar ni, an rufe min zaurena na Tiktok ne, kamar yadda na gano daga baya cewa wasu ne waɗanda ban san su waye ba suka yi ƙarar zauren wanda shi ne ya yi sanadiyyar rufewar da aka yi min, duk don na karaya. Amma na mayar da komai ba komai ba, saboda na san burin su kenan su kai ni ƙasa. A rayuwa dama dole ka samu maƙiya da kuma masoya, in sha Allahu Ubangijina ba zai ba su damar hakan ba. Daga ƙarshe ku dage da addu’a na tabbata da ba don addu’ar da nake ba, da ban kai wannan matakin ba, don na daɗe ina roƙon Allah Ya ɗaukaka ni, sai ɗaukakar ta zo min a lokacin da ban zata ba ban yi tsammani ba.

Tsakanin rubutun littafi da na waƙa wanne ya fi ba ki wahala?

Gaskiya waƙa ta fi bani wahala, saboda tsintar ta kawai na yi daga sama, ba tare da na shirya mata ba.

Shin akwai wani ƙalubale da ki ka taɓa fuskanta a harkar rubutu?

Dama ita rayuwa cike take da ƙalubale. Babu shakka na fuskanci ƙalubale iri-iri daga lokacin da na fara rubutu zuwa yanzu. A farkon rubutuna ba a sani a gida ba, kuma ba komai ya sa na ƙi faɗa ba, don ina fargabar za a hanani ne. Amma a hankali a hankali na fara nuna musu ina yi, kuma Alhamdulillah sun karɓa hannun bibbiyu.

Ƙalubale na biyu kuma shi ne da farko da na fara rubutu sai nake ganin kamar ai ma ba a san da ni ba, ko ba za a sanni ba, duba ga yadda na ga masu karatu basa yin sharhi ko tsokaci kan labaran da nake rubutawa. Sai daga baya na fahimci ai komai lokaci ne. Yanzu kam Alhamdulillahi, sunan Milhart ya yi nisan da ita kanta ba ta san a iya inda ya tsaya ba.

Ya ki ke kallon wannan maganar da ake cewa marubuta suna da girman kai? Shin kin yarda?

Kai tsaye ba zan ce haka ba ne, saboda ni kaina an sha faɗa min hakan, sai daga baya idan mun zauna da mutane sai ki ji suna cewa ashe baki da girman kai, wata har ce min ta yi sun yi gulmana, na yafe musu. Ni a karan kaina idan ban sanka ba ba na shiga harkar ka, wanda na san akwai masu irin wannan halin nawa da yawa. Wasu kuma haka halittar su ce haka, ba su cika son yin magana ba, ko in ce ba sa son surutu. Duk da dai na san ba za a rasa masu girman kan ba, amma idan na ce tabbas akwai ban yi wa marubuta adalci ba, saboda ban tava cin karo da hakan ba.

Yaya ki ke kallon ƙalubalen da harkar rubutun adabi ke fuskanta? Sannan idan aka ce ki ba da shawarar yadda za a kawo gyara a harkar mai za ki ce?

A taƙaice dai shi adabi zan iya cewa hanya ce ta idar saƙo game da zamantakewar al’umma, da nufin faɗakarwa, ilimantarwa da kuma nishaɗantarwa. Abinda kuma zan gyara idan na samu dama shi ne ƙalubalen rubutun batsa da wasu ɓatagari daga cikin marubuta suke yi. Babu shakka hakan yana bada dama wajen ɓata sunan marubuta, da kuma ɓata tarbiyyar yara da ma matasan da ba su san ciwon kansu ba. Sai dai mu ce Allah Ya shige mana gaba, Ya gyara mana kangararrun cikinmu, Ya kuma nufe mu da rubuta alheri da abin da zai dace da koyarwar addinin Musulunci da al’adunmu na Arewa.

Shin a fahimtarki menene ya bambanta marubutan onlayin da kuma marubuta dauri masu mawallafa littattafansu?

Ai bambancin a bayyane yake, babu ma haɗi. Da dama daga cikin marubutan mu na onlayin shirme ya yi musu yawa, suna rubutu ne kawai kara zube, babu kiyaye ƙa’idojin rubutu, kuma ba sa bincike. Kodayake akwai fasihai sosai a cikin mu waɗanda a ko’ina za a kira su da marubuta, saboda yadda suke rubutu cikin tsari da tsafta. Tsofaffin marubuta na baya kuwa suna amfani ne da zallar basira da ƙwarewa. Suna aiki da shawara, suna bincike, da kiyaye dokokin rubutu, kuma da wuya ka samu batsa a cikin rubutunsu, duk da kasancewar da dama a cikinsu su ma sun fara rubutu ne da ƙuruciya.

Su waye marubutan da ki ke yabawa da rubutunsu?

Fauziya D. Sulaiman, Binta Umar Abbale, Shamsiyya Manga, Hadiza D. Auta, Yakubu Yafson Azare.

Wacce ce madubinki a cikin marubuta?

Fauziyya D. Suleiman.

Wanne littafi ne ki ka taɓa karantawa wanda ki ka ji ko za ki karanta shi sau goma ba za ki gaji?

‘Da Wata a Ƙasa’ na Binta Umar Abbale.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

Bayan Wuya Sai Daɗi

Mun gode.

Masha Allah. Ni ce da godiya.