‘Yan bindiga sun halaka ‘yan kasuwa takwas a Katsina

Spread the love

Daga Umar Garba a Katsina

‘Yan bindiga masu tarin yawa dauke da muggan makamai sun tare ayarin motocin ‘yan kasuwa inda suka kashe wasu mutane takwas a lokacin da suka kai wani hari kan ayarin da ke dawowa daga kasuwar garin Yantumaki da ke karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.

A duk mako ‘yan kasuwar kan yi ayari don tafiya cin kasuwa inda suke samun rakiyar jami’an tsaro, sai dai a wannan karon ‘yan ta’addar sun yi wa jami’an tsaron kwanton bauna inda suka jikkata wasu daga ciki suka halaka wasu ‘yan kasuwar.

 Shugaban kungiyar direbobi a yankin, Kabiru Dangaye, ya bayyana cewa wa majiyar Manhaja cewa, ‘yan ta’addar sun bude wuta kan ‘yan kasuwar ne a daidai lokacin da sojoji dauke da makamai suka yi wa ‘yan kasuwar rakiya cikin motoci 25 a ranar Juma’a.

Mutane takwas ne suka mutu nan take sakamakon harin yayin da aka kai wadanda suka jikkata asibiti don kula da lafiyarsu.

Shugaban ya bayyana wa Leadership cewar, “Direban mu sun jira sa’o’i da dama kamar yadda suka saba kafin sauran direbobi da ‘yan kasuwa su zo daga unguwannin makwabta domin fara tafiya.

“Muna da motoci kusan 25 daga nan sai muka kira sojoji su zo su yi mana rakiya kamar yadda muka saba, sojoji suka shiga motarsu.”

Dangaye ya qara da cewa “sun tashi daga Mai Dabino da ke yankin Danmusa, inda suka tashi a cikin ayari, suka wuce Sabon Garin Nasarawa da Mahuta, sai barayin suka yi kwanton dauna a kewayen unguwar Makera.

“’Yan ta’addar sun kasu kashi hudu ne kuma a lokacin da babbar motar ta isa rukuni na uku ne ‘yan ta’addar suka fara harbin. A lokacin da sojoji suke tuki a baya, da nufin tafiya gaba da sauri, sai wasu ‘yan ta’addar suka fara harbe-harbe a kansu, amma sojoji sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi, saboda karfinsu, ‘yan ta’addar sun yi galaba a kan sojoji.” Inji shi.

Dangaye ya kara da cewa an yi kira don a kawo dauki ga tawagar da karin sojoji domin taimakawa ‘yan kasuwar.

Kawo yanzu rundunar ‘yan sanda a jihar bata yi karin bayani ba dangane da lamarin.

By Editor