*Za a gina makarantu tsangaya a mazabun sanata
Daga BASHIR ISAH
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kaddamar da raba kayayyakin aiki ga manoma a shiyyar Zamfara ta Yamma.
Shirin wanda ke mazaunin bangare na tayar da komadar da annobar Korona ta haddasa wa Nijeriya da kuma yaukaka tattalin arziki karkashin Shirin FADAMA III, an kaddamar da shi ne a yankin Karamar Hukumar Gummi da ke jihar.
Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa, Gwamna Lawal ya kaddamar da shirin rabon kayayyakin ne hadi da gina Makarantar Tsangaya irin ta zamani a yankin na Gummi.
Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta amnice da gina Makarantar Tsangaya ta Islamiyya a daukacin mazabar sanata guda ukun da Zamfara ke da su domin inganta sha’anin ilimi.
“Shirin yankin Karamar Hukumar Gummi na da zummar bunkasa manoma a mazabar sanata ta Zamfara ta Yamma,” in ji Idris.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Gwamna Lawal ya ce shirin na da himmar gina sabbi da gyara tsaffin hanyoyin karkara a sassan jihar.
Ya ce, “Gwamnatina za ta tabbatar da gyara kasuwannin danyun amfanin gona da gina sabbi tare da inganta su.
“Babban burinmu shi ne, bunkasa manoma ta hanyar samar musu da ingantattun kayan aiki irin su takin zamani, magungunan kashe ciyayi da kwari, ingantaccen iri da magungunan killace iri.
“Dangane da noman rani kuwa, mun raba buhun takin zamani guda 33,000 wanda ya hada da NPK buhu 22,000 da Urea buhu 11,000.
“Wannan kari ne a kan ‘power tillers’ sama da 700 da kuma irin shinkafa da na masara da muka raba wa manoma 19,000.
“Kungiyoyin manoma 735 ne za a tallafa wa da ‘Power Tillers’, yayin da mutum 2,550 za su samu irin dabbobin kiwo,” in ji Gwamnan.
