Almundahana: Yadda EFCC ke ƙoƙarin titsiye tsofaffin jami’an Buhari mata

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A cikin makon nan ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Shugabar Hukumar Shirin Bada Tallafi da Dogaro da Kai, wato ‘National Social Investment Programme Agency’ (NSIPA), inda a gefe guda kuma tun a makon jiya Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta mika goron gayyatarta ga tsohuwar Ministar Jinkai da Agaji a lokacin tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, wato Sadiya Farouq kan zargin ta da hannu a badakalar Naira biliyan 37.1.

A bangaren Halima Shehu ta hukuma NSIPA, wacce ke karkashin Ma’aikatar Jinkan, bayanai sun ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta soma tutsiye ta a ranar Talata bayan da jami’an hukumar suka dira a ofishinta tare da gudanar da bincike, daga bisani kuma ta isa ofishin EFCC, inda suka yi ma ta tambayoyi har cikin dare.

Sai dai daga bisani Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta dakatar da Halima Shehu bayan amincewa da nadin Dokta Akindele Egbuwalo don maye gurbinta a matsayin mukaddashi. Dokta Akindele Egbuwalo, shi ne kodinetan shirin N-Power na kasa, kuma sabon nadin nasa ya fara aiki nan take.

Hajiya Halima Shehu a baya ta tava aiki da ma’aikatar jinkai ta tarayya daga 2017 zuwa 2022.

Rahotanni sun ce shugabar ta NSIPA da aka dakatar na shirin gudanar da taron manema labarai ne a ranar Talata, lokacin da jami’ai daga hukumar EFCC suka je ofishinta a birnin Abuja.

Jaridar Punch ta ambato wata majiya na cewa an samu rashin jituwa tsakanin Halima Shehu da ministar jinkai ta yanzu, Dr. Betta Edu tun lokacin da ta kama aiki saboda zargin cewa zikau ita kadai tana yin amfani da kudaden hukumar wadanda aka tanada don bayar da tallafi ga kungiyoyin jama’a masu rauni.

An kafa shirin ba da kwarewar dogaro da kai ne don tallafa wa miliyoyin ‘yan Nijeriya su fita daga cikin talauci da inganta harkokin cudanyar al’umma da kuma samar da sana’o’i ga talakawa da ‘yan kasa masu rauni.

Hukumar ce kuma ke da alhakin kula da shirye-shiryen yaki da talauci kamar shirin ciyar da dalibai ‘yan makaranta na kasa.

An ambato Halima Shehu a baya-bayan nan yayin wani taron manema labarai a Abuja, tana jaddada kudurinta na tabbatar da gaskiya wajen aiwatar da shirin ba da tallafin kudi Dala miliyan 800 na Bankin Duniya.

Ita kuwa tsohuwar ministar Buhari, Sadiya Farouq, rahotanni sun nuna cewa ba ta je wajen gayyatar da EFCC ta yi ma ta ba, saboda halin rashin lafiya kamar yadda majiyar EFCC din ta ruwaito.

A cewar majiyar, tsohuwar ministar, ta nemi EFCC ta kara ma ta lokaci, saboda dalilai na rashin lafiya.

Tun farko, kafofin yada labaran Nijeriya sun ruwaito cewa tsohuwar ministar ba ta bayyana a hedikwatar hukumar ta EFCC ba.

A farkon makon jiya ne, Sadiya Umar Farouq ta fitar da wata sanarwa, wadda a ciki ta musanta hannu a badakalar da ake zargi. Ta ma yi ikirarin cewa kwata-kwata ma ba ta san dan kwangilar da rahotanni ke cewa hukumar EFCC ta kama a binciken da take yi dangane da batun ba.

Wata majiya daga EFCC a ranar Laraba ta tabbatarwa da manema labarai cewa hukumar na sa ran isar tsohuwar ministar ta zamanin Shugaba Muhammadu Buhari, zuwa ofishinsu da ke Abuja.

Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’an EFCC sun shafe tsawon sa’o’i suna dakon isar Sadiya Farouq, amma har lokaci ya kure ba su ga tsohuwar ministar ba, kuma ba tare da samun wani bayani daga gareta a kan dalilinta na gaza bayyana a hukumar ba.

EFCC dai ta gayyace ta ne tun a makon jiya domin ta yi qarin haske game da zargin halasta kudin haram a karkashin shugabancinta.

A sakon da ta wallafa a shafinta na X, tsohuwar ministar ta ce “Akwai rahotanni da dama da ke alakanta ni da wani bincike na hukumar EFCC game da ayyukan wani James Okwete, kwata-kwata ma ni ban san shi ba.”

A cikin Disembar 2023 ne masu cin gajiyar shirin N-Power suka gudanar da zanga-zanga kan kin biyansu alawus da aka dauki tsawon watanni ba a yi ba tun kafin tsohuwar gwamnati ta shude.

By Editor