Akwai buƙatar kowa ya sa hannu wajen farfaɗo da ilimin firamare a Zariya – Dr. Hassana

Daga ISAH GIDAN ƁAKKO a Zariya

Sakatariyar Ilimi ta Karamar Hukumar Zariya, Dokta Hassana Muhammad Lawal ta bayyana kudurinta na bin duk hanyoyin da su ka dace domin kawo karshen matsalolin da suke addabar makarantun firamare a karamar hukumar Zariya.

Dr. Hassana Lawal ta bayyana haka ne a jawabin da ta yi a lokacin dora dambar makarantun firamare da suke qaramar hukumar Zariya, inda ta fara da makarantar firamare ta Zage-zagi a birnin Zariya.

Dr. Hassana ta bankado matsalolin da su ke addabar makarantun firare a karamar hukumar Zariya da suka hada da gine-ginen gidaje da sauran gine-gine da al’umma ke yi a harabar makarantun da yawan sace-sace a makarantun da kuma rashin kafa kungiyar iyaye da malamai da kuma rashin kwamiti mai karfi (SBMC) a mafiya yawan makarantun firamare da sue karamar hukumar Zariya.

A kan haka, ta jawo hankalin daukacin al’ummar wannan karamar hukuma, ko da yaransu ba su a makarantun firaremare na gwamnati, da su tashi tsaye wajen ganin sun hada hannu da sashin ilimi na karamar hukumar Zariya domin a cewarta a samu saukin warware matsalolin da suke addabar makarantun da suke karamar hukumar Zariya.

Shi ko tsohon magatakatdar hukumar bunkasa harshen Larabci da addinin Musulunci Farfesa Muhammad Shafi’u Abdullahi ya nuna matukar jin dadinsa da Ziyarar da Dr Hassana Lawal ta kawo ziyara wannan firamare ta Unguwar Zage-zagi, inda ya ce al’ummarsu na shirye su ba da duk goyon bayan da ta ke bukata.

Wakilin makarantan Zazzau wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Jama’atul Nasrul Islam a jihar Kaduna ya kara da cewar wajibi ne in al’umma na son ci gaba a rayuwar ta, wajibi ne kowa da dan siyasa ga mai sarauta da masana ilimi da kuma sauran al’umma su ba sakatariyar ilimi duk goyon bayan da ta ke bukata, a cewarsa, gyaran da ta ke son yi na al’ummar karamar hukumar Zariya ne ba na ta ba.

A dai lokacin wannan ziyara da Sakatariyar Ilimi a karamar hukumar Zariya Dokta Hassana Muhammad Lawal  ta za ga harabar wannan makaranta, inda ta gane wa idon ta matsalolin makaratar tare da alkawarin irin wannan ziyara za ta ci gaba da yi a daukacin makarantun firamare da suke karamar hukumar Zariya.