Iyalan da ‘yan bindiga suka kashe sun samu taimakon gwamnatin Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta kashe Naira miliyan 120 wajen tallafa wa iyalan da ‘yan bindiga suka kashe a jihar.                                                       

Mai ba gwamna shawara akan ‘yan gudun hijira Sa’idu Ibrahim Danja wanda ya sanar da haka ya ce wannan kudi an yi amfani da su ne wajen tallafawa marayu da aka kashi masu iyaye sanadiyyar hare-hare na ‘yan bindiga a jihar.

Mai ba gwamnan shawara ya sanar da haka ne a wata liyafar da wasu aminansa suka shirya masa a Katsina.                                                  

Ya ce wannan tallafi da gwamnti ta bada zai taimaka marayun wajen rage masu radadin halin kuncin da suka samu kansu na wani lokaci.       

Sa’idu Ibrahim Danja ya jadda kudirin gwamnati Dikko Radda na samar da da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.        

Sai ya yi kira ga al’ummar jihar su ci gaba da bada goyon bayan su tare da addu’ar samun zaman lafiya a jihar da kasa baki daya.

By Editor