Emefiele: EFCC ta kai wa Ɗangote sumame bayan rikitowarsa a matsayin attajirin Afirka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jami’an Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati, EFCC, a ranar Alhamis, sun kai samame babban ofishin Kamfanin Dangote dake Legas. Kamar yadda shafin jaridar TheCable ya rawaito, jami’an hukumar sun gudanar da bincike kan kudaden da aka ware wa kamfanin a zamanin Godwin Emefiele, tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya CBN. Amma Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya qi cewa komai kan batun.

Sai dai wani ma’aikacin Kamfanin Dangote ya tabbatar da cewa, jami’an EFCC na nan a babban ofishin kamfanin. “Sun bukaci a ba su takardu kan hada-hadar kudi da CBN,” inji ma’aikacin.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Dangote ya fado a matsayin attajirin da ya fi kowa kudi a Afrika.

Mujallar Forbes da ke bibiyar harkokin masu arzikin duniya, ta ce a yanzu hamshakin biloniyan nan dan kasar Afirka ta Kudu, Johann Rupert ne mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka.

Hakan na nufin Johann Rupert mai shekara 73, ya kere attajirin dan kasuwa na Nijeriya, Aliko Dangote a yawan arziki wanda a baya yake rike da matsayin.

A alkaluman da Forbes ta fitar na baya-bayan nan kan arzikin attajirai a kowacce rana, darajar arzikin Johann Rupert ya kai Dala biliyan 10, yayin da Aliko Dangote aka kiyasta nasa arzikin a kan dala biliyan 9.7.

Aliko Dangote, mai shekara 66, ya koma mataki na biyu a jerin masu arzikin Afirka bayan da dukiyarsa ta yi kasa daga Dala biliyan 13.5 zuwa dala biliyan 9.5 a farkon shekarar 2024.

Mujallar ta nuna cewa an samu raguwar kudin hamshakan ’yan kasuwa, kamar Abdussamad Rabiu, wanda darajar arzikinsa ya kai Dala biliyan 5.7 da Mike Adenuga, wanda nasa arziqin ya kai Dala biliyan 3.1.

Bayanai na cewa raguwar darajar arzikin nasu, ba zai rasa nasaba da yadda darajar Naira ke cigaba da faduwa ba da kuma wasu matsaloli da suka shafi tattalin arziki.