Za mu noma hekta 500,000 don bunƙasa abinci da sauƙaƙa shi a Nijeriya -Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta noma hekta 500,000 domin bunkasawa, wadatarwa da saukaka kayan abinci a fadin Nijeriya.

Tinubu bayyana haka a cikin jawabin sa na murnar shiga sabuwar shekarar 2024, wanda ya yi a safiyar Litinin.

“Za mu noma hekta 500,000 a fadin kasar nan domin samun masara, shinkafa, alkama, gero da sauran kayan abincin da zai wadaci ‘yan Nijeriya,” inji Tinubu.

Cikin watan Nuwamba ne dai Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin noman alkama a Jihar Jigawa, shirin da manoma 250,000 za su ci gajiyar noman alkama a Jigawa.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta tallafa wa kama daga kananan manoma 150,000 zuwa 250,000 da tallafin kashi 50 bisa 100 na kayan noma, domin samun damar noma hekta 200,000 zuwa 250,000, a wani gagarimin Shirin Noman Alkama a tsarin noman rani a Jihar Jigawa.

Ana sa ran samun alkama mai yawan tan 1,250,000.

Ministan Harkokin Noma da Bunkasa Kayan Abinci, Abubakar Kyari ne ya bayyana haka, tare da cewa an bijiro da shirin domin rage tsadar kayan abinci da kuma rage dogaro da shigo da kayan abinci daga wajen kasar nan.

Kyari ya kara da cewa wani dalilin kirkiro shirin kuma shi ne domin a samar da wadataccen abinci a cikin kasa.

Da ya ke magana a Hadeja, yayin kaddamar da Shirin Bunkasa Noman Alkama Cikin Rani, ya ce za a tabbatar cewa tallafin kayan noman zai iya ga mutanen da za a raba saboda su.

“Noman rani ya na ba mu gagarimar dama ta cin moriyar wawakekiyar kasa da albarkatun da ke cikin ta, wajen bunkasa noma domin samun wadataccen abinci.”

Ya ce bayan ga noman damina da jama’a ke yi, wata hanya ta samar da abinci mai tarin yawa, ita ce noman rani, wanda har tattalin arzikin kasa ya ke bunkasawa.

Ya ce Shirin Bunqasa Noman Alkama a Lokacin Rani ya na karkashin Shirin NAGS-AP, wanda Gwamnatin Tarayya za ta gudanar daga lamunin dala miliyan 134 da aka ciwo a Bankin Bunkasa kasashen Afrika, wato AfDB.

Kyari ya ce shirin na daga cikin muradun Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ganin ana kara samun yawaitar jajirtattun manoma wadanda za su bada himma sosai wajen noman irin su alkama, shinkafa, masara da rogo a fadin kasar nan.

Ministan ya ce a karkashin wannan shiri, za a bai wa noman dawa, waken soya a lokacin damina.

“Manoman kasar nan sun kasance su ne jari mafi tsadar da wannan kasa ke tutiya da su a ko da yaushe. Saboda su ne ke wadatar da su da abincin da mu ke ci a kasar nan.