Zargin $6.2m kan Emefiele: Boss Mustapha ya bayyana a kotu don wanke kansa

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

An gabatar da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, a Babbar Kotu mai zamanta a Abuja dangane da shari’ar tsohon Gwanan CBN, Godwin Emefiele da ke gudana.

An gurfanar da Emefiele a gaban Mai Shari’a Muazu ne kan sabbin tuhume-tuhume guda 20 da suka hada rashawa, hadin baki, amfanin da bayanan karya wajen karbar makudan kudi har $6,230,000 da sauran su.

Kazalika, tuhumar ta hada da yin shigar burtu a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya wajen karbe kudi $6.2m ba bisa ka’ida ba.

Da yake ba da bahasi a gaban kotu game da zargin badakalar miliyan $6.2, Mustapha ya ce har ya zuwa loakcin da ya bar ofis bai san komai game da wannan hadakalar ba.

Ya kara da cewa, yana da yakinin  a tsakanin shekara biyar da watanni bakwai da ya yi aiki, takardun bayanan da ake batu ba daga ofishinsa suka fito ba.

A zaman da kotun ta yi a ranar Litinin, wani shaida mai suna Onyeka Ogbu, ya bada bayanin yadda tsohon Gwamnan CBN ya amince da biyan tsabar kudi  $6,230,000 ga masu sanya ido a harkar zabe na kasa da kasa yayin zaben 2023.

Haka shi ma Mustapha, ya bayyana a kotun a ranar Talata inda ya nuna wa kotun cewa ba shi da masaniya dangane da biyan kudaden da ake batu.

By Editor