Daga BASHIR ISAH
Alamu bayyanannu na nuni da cewa, akwai yiwuwar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sanar da sabon albashi mafi ƙaranci a ranar 1 ga watan Mayu mai zuwa.
Kuma zai yi hakan ne albarkacin bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya wanda akan gudanar a ranar farko ga watan Mayu duk shekara.
Majiyarmu ta ce, Kwamitin Albashin na Ƙasa na aiki tukuru don tabbatar da an cimma dukkan sharuɗɗan da aka shimfiɗa dangane da sabon albashi mafi ƙarancin.
Majiya ta kusa da kwamitin ta ce, “Kwamitin Albashi zai sake zama ya zuwa makon gobe. Zama ne wanda kwamitin zai karɓi rahotanni daga tarurrukan jin ra’ayi da aka shirya a sassa daban-daban wanda hakan zai daidaita wa Kwamitin alƙibla dangane da aikin da ke gabansa.”
Majiyar ta ƙara da cewa, “Bayan Kwamitin ya kammala tattara bayanansa, daga nan zai yi la’akari da matsayar ƙungiyoyin NLC, TUC da NECA kafin daga bisani a cimma matsaya guda game da sabon mafi ƙarancin albashin.
“Za mu yi ‘yan sauye-sauye, kuma ina da yaƙinin kwamitin zai yi zama da Shugaban Ƙasa don duba yiwuwar fara aiwatar da sabon albashin. Haka kuma zai yi zama da gwamnonin jihohi,” in ji majiyar.
Majiyarmu ta ce, ƙoƙarin da ta yi don jin ta bakin Ministan Yaɗa Labarai kan wannan batu, ya ci tura.
Bugu da ƙari, wata majiya ta kusa da Shugaban Ƙasa wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaida wa majiyarmu cewa, wataƙila Shugaba Tinubu ba zai jinkirya zuwa 1 ga Mayu ba wajen sanar da sabon albashin.
