Wasu mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon turmutsitsin da ya auku a wajen raba wa jama’a zakka a jihar Bauchi.
Lamarin ya faru ne ranar Lahadi da misalin ƙarfe 12 na rana a harabar hedikwatar kamfankn Shafa Holdings Company plc da ke hanyar Jos a jihar.
MANHAJA ta kalato cewa, wani matashi da ya jikkata a wajen turmutsitsin na kwance a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi ana yi masa magani.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ahmed Wakili, ya tabbatar da aukuwar haka ga jaridar News Point Nigeria.
