Gwamna Abba ya umarci a biya kuɗaɗen ’yan shara cikin gaggawa

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

A yanayin damuwa kan cece-kuce da ake yi da kuma iƙirari na ƙin biyan kuɗaɗen alawus-alawus na masu shara, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin biyan ma’aikatan cikin gaggawa.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Gwamnan ya yi wata ganawa ta musamman da ma’aikatan kwashe sharar da shuwagabanninsu a makon nan a ɗakin taro na Coronation dake fadar gwamnati.


Gwamna Abba Yusuf ya umarci ma’aikatar muhalli da kula da tsaftar muhalli (REMASAB) da ta tabbatar da biyan duk wasu kuɗaɗen alawus-alawus na masu shara da suka gada daga gwamnatin da ta gabata.

Sannan Gwamnan Abban ya ƙaryata jita-jitar da ke tada ƙayar baya na shirin gwamnati na korar masu sharar tituna da suka gada daga gwamnatin da ta gabata, inda ya qara da cewa ba shi da niyyar hana ma’aikatan da ba su yi aiki ba su samu abin dogaro da kai.

Abba Kabir wanda ya bayar da wannan umarni a ranar Lahadin da ta gabata yayin wata ganawa da wakilan masu shara a gidan gwamnati, ya nuna rashin gamsuwa da dalilin da ya sa ake jinkirin biyan wasu kuɗaɗen da ake ci gaba da yi bayan amincewarsa.

“Bari na bayyana hakan, ban kuma ba da umarnin korar ɗayan ku a nan ba saboda wani dalili, maimakon haka mun ɗauki ƙarin ma’aikata domin muhallinmu ya kasance cikin tsafta.

A matsayin mu na ‘yan ƙasa nagari. na jiha wace fa’ida zan ji daɗin sallamar ku daga abinda ke samun abincin yau da kullum.

“Wannan taron ya zama wajibi bisa la’akari da kukan da ake yi a kai a kai da kuma takaitaccen bayani mara daɗi da na ke samu kan rashin biyan ku alawus-alawus ɗin ku, ina mai tabbatar muku da cewa za ku karɓi alawus ɗin ku da wuri-wuri, mun gano inda matsalar take da kuma inda matsalar take kawo ƙarshen matsalar.”

Da yake yaba musu bisa haƙuri da jajircewarsu wajen gudanar da ayyuka, ya buƙace su da su ci gaba da baiwa gwamnati riƙon amana da aiki tuƙuru, inda ya ce za a rinqa tura su na unguwannisu don kada su yi nisa da yankunansu.

Don haka Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana shirin gwamnatinsa na sayen manyan motocin (Bocket lifters) domin sauƙaƙa kwashe sharar ba kawai daga tituna ba har ma daga lunguna da saƙo na jihar.

By Editor