Sarkin Musulmi ya ƙaddamar da Cibiyar Ilimin Al-Ƙur’ani ta tsangaya a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD, a  Gusau

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alh Sa’ad Abubakar III ya kaddamar da cibiyar koyar da Al-Kur’ani ta jihar Zamfara a ranar Lahadi a garin Gummi, hedikwatar karamar hukumar Gummi ta jihar.

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sanya wa cibiyar sunan Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III cibiyar ilimin Kur’ani mai tsarki.

Da yake jawabi a lokacin kaddamar da aikin, Sultan Sa’ad Abubakar ya yaba wa Gwamnatin Zamfara bisa wannan sabuwar dabara.

A cewarsa, cibiyar za ta magance barace-barace a tsakanin almajirai da Kuma bai wa almajiran makarantun allo samun damar yin ilimin boko.

Basaraken ya yi kira ga Gwamnatin Jihar da ta tabbatar da dorewar shirye-shiryen.

A nasa jawabin Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa, an gina cibiyar a gundumomi uku na ‘yan majalisar dattawan jihar da nufin ganin an shigar da daliban makarantun allo cikin tsarin ilimin Alkur’ani da na zamani a jihar.

A cewarsa, cibiyoyin suna karkashin shirin Bankin Duniya ne tare da da hadin gwiwa da hukumar kula da ilimin bai-daya ta kasa, yana mai bayyana cewar, makarantun za su ci gaba da gudanar da ayyukansu a karkashin hukumar ilimi bai-daya ta ZMSUBEB domin dorewar shirin.

Ya kara da cewa, an samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da rijiyoyin burtsatse da dakunan kwanan dalibai guda tara da dakunan ma’aikata da kuma kayayyakin koyo da koyarwa na Musulunci da ilimin zamani a hade.

Daga nan, Gwamna Dauda ya yi kira ga al’ummomin da suka amfana da shirin da su tallafa wa shirin ta hanyar sanya ‘ya’yansu a makarantun tare da kare makarantun daga barna domin amfanin su.

A yayin taron, gwamna Dauda Lawal ya kaddamar da sabon gidan man fetur da aka gina a wajen Gummi, da da Babban asibitin na garin Nasarawa Burkullu a karamar hukumar Bukkuyum da kuma duba ayyukan gyare-gyare da sake ginawa a asibitin karamar hukumar Maru.

By Editor