An maka gwamnonin Nijeriya a kotu kan rashin sakar wa ƙananan hukumomi mara

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta maka Gwamoni 36 na Jihohin Nijeriya a Kotun Ƙoli kan tauye haƙƙoƙin Shugabannin Ƙananan Hukumomi.

Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Lateef Fagbemi ne ya tabbatar da hakan.

Lateef ya ce, Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar ƙwato wa shugabannin ƙananan hukumomi ‘yancinsu a hannun gwmanoni, tare da ba su cikakken ikon cin gashin kansu.

Kazalika, Gwamnatin ta kuma buƙaci Kotu da ta bayar da umarnin haramta wa gwamnoni sauke zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi ba bisa ƙa’ida ba.

Ta kuma buƙaci Kotun ta ba damar da za a tiƙa tura wa ƙananan hukumomin kuɗaɗen kai-tsaye daga asusun gwamnatin ƙasa daidai da tanadin kundin mulkin ƙasa saɓanin amfani da asususn tarayyar da gwamnonin suka ƙirƙiro.

Sai kuma batun kafa kwamitin riƙon-ƙwarya don jan ragamar ƙamar hukuma wanda Gwamnatin ta nemi Kotun da ta haramta wa gwamnonin daga yanzu, da dai sauran buƙatu.

A hin da ake ciki dai, Kotun ta ayyana ranar 30 ga watan Mayu don fara sauraren wannan ƙarar.

By Editor