Ana fagarbar mutane da dama sun mutu sakamakon ruftawar masallaci a Legas

Spread the love

Ana fargabar mutane da dama sun mutu sanan wasu da ya yawa sun jikkata sakamakon ruftawar ginin masallaci wanda ya auku Papa Ajao, Jihar Legas.

Bayanai sun ce ruftawar da auku ne ranar Lahadi yayin da masallata ke tsaka da sallar Azahar.

Manhaja ta kalato cewar, an gano wasu gawarwaki da ma waɗanda suka suka jikkata a ƙarƙashin ɓuguzan ginin, kuma ana fargabar akwai wasu da dama da suka maƙale.

Ya zuwa kammala haɗa wannan labari, babu wani bayani a hukumance a kan lamarin.

By Editor