Gwamnatin Tinubu na goyon bayan bai wa ƙananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai – Akume

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya bayyana cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ta na goyon bayan a bai wa ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar nan ‘yancin cin gashin kan su, kai-tsaye daga asusun gwamnatin tarayya.

Akume ya bayyana haka lokacin da yake wa manema labarai jawabi bayan kammala taron Majalisar Zartaswa a ranar Laraba, a Abuja.

An yi taron domin tattauna cikar Gwamnatin Tinubu shekara ɗaya da kafuwa.

Akume ya ce Shugaba Tinubu ya maida hankali sosai wajen bin doka da oda da tsarin mulkin ƙasa tun da ya hau mulki.

Ya ce Tinubu ya yi alwashin ci gaba daga inda gwamnatin da ta gabata ta tsaya a ƙoƙarin ganin an bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kansu.

“A batun nema da kiraye-kirayen a yi taron ƙasa don a tattauna batun cin gashin kan ƙananan hukumomi, ina ganin Majalisar Dattawa ta yi kooƙari sosai.”

“Wannan gwamnatin ita ma ta na goyon bayan wannan batu, kuma za mu ci gaba da ƙoƙarin ya tabbata a ƙasar nan.”

Ya ce wannan gwamnati ta yi amanna cewa ƙananan hukumomi sun fi sauran gwamnatocin tarayya da jihohi kusanci da jama’ar yankunan karkara.

Ya ce sai dai kuma duk da haka akwai gwamnonin jihohi waɗanda su ke da ‘yancin karɓar kuɗaɗe daga Asusun Gwamnatin Tarayya.

Makonni biyu da suka gabata ne dai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin ya ce Gwamnoni sun kashe ƙananan hukumomi, su na karkatar da kuɗaɗen su ba bisa ƙa’idar doka ba.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya jaddada cewa gwamnoni na karkatar da kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke bai wa ƙananan hukumomi suna sha’anin gaban kan su da kuɗaɗen.

Barau ya bayyana haka a ranar Laraba, yayin da ya shugabanci zaman majalisar dattawa.

Ya furta haka ne bayan Sanata Kawu Sumaila na NNPP daga Kano ya kawo ƙorafin buƙatar a bai wa kowace ƙaramar hukuma cin gashin kanta.

Sanata Jibrin ya ce tabbas wasu gwamnoni su na ƙananan hukumomi illa sosai, saboda son zuciyar su.

Ya ce gwamnoni su na kamfatar kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke bai wa ƙananan hukumomi, lamarin da Barau ya ce zamba ce.

“Tsarin ƙananan hukumomi ya mutu murus, saboda kuɗaɗen da tarayya ke ba su, akasari duk gwamnoni ke karkatar da su.

“Za a ce ku je ku rubuto kuɗaɗen da ku ke buƙata, daga nan sai gwamna ya daddatsa kuɗaɗen ya kamfaci iya son ran sa.”

Amma fa ban ce haka dukkan gwamnoni ke yi ba. Akwai gwamnoni mutanen kirki, waɗanda ba su yin hakan. Amma wasu da na aikata hakan.” Cewar Barau.

Ya ce hanyar da za a iya bai wa ƙananan hukumomi cin gashin kan su.

Hakan kuwa ba zai yiwu ba sai an shigar da dokar cikin Kundin Dokokin Najeriya.

Daga nan ya jinjina wa gwamnonin da ba su cirar kuɗaɗe daga asusun ƙananan hukumomi, sannan ya yi kira gwamnonin da ke cirar kuɗaɗen su daina.

By Editor