CISLAC ta yi kira a wanzar da zaman lafiya a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisun Dokokin da Yaƙi da Rashawa a Nijeriya (CISLAC), ta bayyana damuwarta game da abubuwan da ke faruwa a Kano dangane da batun sauya sarki a jihar.

CISLAC ta yi gargaɗin cewa irin abubuwan da ke faruwa a jihar ta Kano na barazana ga zaman lafiyar jihar.

Babban Darakta a cibiyar, Auwal Musa Rafsanjani, ya fitar da tsattsauran gargaɗi a kan duk wani yunƙuri na amfani da yanayin da ake ciki a jihar domin ayyana dokar ta ɓaci,

Ya ce, ” Irin waɗannan ayyuka ana kallonsu ne a matsayin ganganci da kuma takalar faɗa na babu gaira babu dalili da janyo ɓata shekara 1000 na tarihin siyasar jihar”.

CISLAC, ta lura cikin fargaba cewa, matsayin kotun wanda hukumomin tsaro suka dogara da shi shi ne ya janyo dawowar sarki Aminu Ado Bayero mai cike da taƙaddama.

Sanarwar cibiyar ta ce, gwamnatin jihar ce kundin tsarin mulki ya ba wa damar naɗi da kuma tabbatar da sarakunan gargajiya ciki har da Sarki.

“Zaman lafiya da cigaban jihar Kano daidai yake da zaman lafiya da cigaban Arewacin Nijeriya, wannan hali da ake ciki ƙoƙarin maida hannun agogo baya ne.

“Don haka CISLAC take kira da a gaggauta samar da yanayin zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a jihar Kano,” inji Rafsanjani.

By Editor