Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Mamallakin rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ƙungiyoyin masu aikata laifuka na cikin gida da waje, waɗanda ya bayyana a matsayin “mafiya”, suna yunƙurin yin zagon ƙasa a aikin matatar man da ya kai Dala Biliyan 19 a Legas.A yayin da ya ke jawabi a taron shekara-shekara na Afreximbank, Aliko Dangote ya ce, ƙungiyar mafia masu safarar mai sun fi ƙarfin masu safara miyagun ƙwayoyi, waɗanda su ne ke neman riƙe masa masana’anta.“To, na san cewa akwai fitina. Amma ban san cewa mafiyan man fetur sun fi ƙarfin mafiyan ƙwayoyi ba. Na tabbatar da haka,” inji shi.Dangote, wanda ya bayyana kansa a matsayin wanda zai kare kansa, ya ce “sun yi yunƙuri iri-iri don hana shi.”Amma ni mutum ne da na kwatar wa kai na ‘yanci a duk rayuwata. Don haka ina tsammanin wani ɓangare ne na rayuwata yin kare kaina,” inji shi.Dangote ya kuma bayyana shirinsa na karkata zuwa ɓangaren ƙarafa, da nufin yin amfani da ƙarafan da ake samarwa a Nijeriya kadai, da kuma samun dogaro da kai.Kwanan nan matatar Dangote ta sake tsara shirin fara sayar da man fetur zuwa ranar 10-15 ga watan Yuli, inda ta mayar da manufarta ta watan Yuni saboda ƙananan al’amurra na kayan aiki.
