Shekaru bakwai da buɗe zauren marubuta a WhatsApp 

Spread the love

A ƙarshen makon da ya gabata na samu zarafin halartar wani babban taron marubuta da aka gudanar a Birnin Kano, ƙarƙashin Zauren Marubuta na manhajar WhatsApp, wanda ya kasance haɗakar marubuta littattafan Hausa, manazarta da ‘yan jarida, malaman harshen Hausa da mawaƙa, da ma duk wani mai ruwa da tsaki a harkar adabin Hausa.

Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta MOPPAN, kuma Sarkin Mawallafan Arewa, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON, wanda bayan kasancewarsa jarumin finafinan Hausa kuma marubuci, ya kasance uba ga marubutan Hausa na Arewa.

Daga cikin dalilan da suka sa aka shirya wannan taro akwai samar da muhallin da marubuta za su haɗu da juna a yi musanyar zumunci da ganawa da sabbin fuskoki da waɗanda aka daɗe ba a haɗu. Sannan taron ya yi daidai da cika shekaru bakwai da buɗe zauren Marubuta a manhajar WhatsApp, wanda kamar yadda na fara bayani a baya ya haɗa dukkan masu ruwa da tsaki a harkar raya adabin Hausa. Harwayau kuma, a yayin taron an ƙaddamar da littafin da aka sanyawa suna, ‘Abin Cikin Ƙwai’, wanda ya ƙunshi gajerun labarai da zauren yake gabatarwa a matsayin gasa a tsakanin mambobin gidan, da kuma fitattun labaran da gwarazan gasar Hikayata ta BBC Hausa na shekarar 2023 suka ɗauki nauyi.

Babu shakka taro ya ƙayatar sosai, ganin yadda marubuta daga sassan arewacin ƙasar nan, maza da mata, suka samu damar halarta. Ciki har da manyan marubuta da suka daɗe suna ba da gudunmawa a harkar rubutun adabi, kuma kowanne taron marubuta aka kira ba sa ƙasa a gwiwa suna ƙoƙarin halarta.

A cewar marubuciyar littafin ‘Amfanin Fitila’, Hadiza D. Auta, a duk cikin zaurukan marubuta da ke onlayin, babu kamar zauren Marubuta, wanda ya haɗo marubuta daga ƙungiyoyin marubuta daga jihohi daban-daban. A taƙaice kenan za a iya cewa zauren shi ma ya zama kamar tumbin giwa, kowacce jiha ko ƙungiya tana da wakilci a ciki. 

Jagoran Zauren Marubuta Bamai Dabuwa marubucin littafin ‘Koren Jaki’ cewa ya yi, ba marubuta kaɗai ne zauren ya haɗa ba, har ma da wasu ƙwararru da suka fito daga ɓangarori daban-daban, irinsu likitoci, lauyoyi, malamai, da manazarta. Kuma shi ne zauren da ya tattaro marubuta daga wasu sassan nahiyar Afirka, kamar su Nijar, Ghana, da Cadi, waɗanda suka zama kamar ’yan uwa na gida ɗaya ko gari ɗaya. A cewarsa, babu wani zaure da ya samu nasarar haɗa marubuta da basu damar taimakawa juna kamar zauren Marubuta. 

Bamai Dabuwa na ganin zauren ya ciri tuta wajen gogar da marubuta da suke shiga manyan gasannin marubuta, saboda horon da ake basu na sanin dabarun rubutun gajerun labarai. Har ma yana cewa, tun da aka fara shirya gasar Hikayata ta BBC Hausa kusan duk waɗanda suka yi nasara a gasar mambobin zauren Marubuta ne! Nana Aicha Hamissou Abdoulaye marubuciyar Hausa daga ƙasar Nijar wacce ta taɓa zama gwarzuwar Gasar Hikayata ta BBC Hausa a 2021, ta ƙara da cewa, har gwarazan gasar Gusau Institute da ta Ɗangiwa da aka samu a baya duk daga zauren Marubuta suke! 

Nana Aicha ta ƙara da cewa, zauren ya haifar da kyakyawar alaƙa tsakanin marubuta maza da mata ta yadda wasu sun zama ƙawaye, wasu aminai, yayin da alaƙar wasu ta rikiɗe ta zama ‘yan uwantaka, har ma da waɗanda suka yi auren a tsakanin su.

Ta ce, ni ma a dalilin wannan zaure akwai mutanen da muka shaƙu da su sosai har ina jin mun zama tamkar ’yan uwa na ciki ɗaya. 

Ta kuma fallasa cewa, bayan romon ilimi da mambobin zauren suke sharɓa, har da tukwicin kuɗi ake basu yayin gabatar da wasu shirye-shirye da zauren ke tsarawa, irinsu ‘Muhawara’, da ‘Wasa Ƙwaƙwalwa’. Akwai kuma gasar rubutun gajeren labari ta wata-wata da ita ma ake bayar da tukwicin har Naira dubu biyar.

Malam Nura Isma’il Abubakar, wanda aka fi sani da Abou Outhaymeen marubucin littafin ‘Ƙarshen Alewa’ na daga cikin jajirtattun marubuta da suke taimakawa wajen kula da al’amuran da zauren ke gudanarwa. Ya bayyana cewa, babu shakka akwai abubuwa da dama da zauren zai yi alfahari da su a tsawon shekaru bakwai da ya yi, daga ciki akwai samar da abubuwa na cigaba da yawa, kamar ɓangaren koyar da yadda za a inganta rubutun adabi, zamantakewa, da ma harkokin addini. Sannan akwai shirye-shirye da zauren ke gabatarwa na cigaban adabi, kamar shirin ‘Tunaninka Kamanninka’, da ake nazari kan kiyaye ƙa’idojin rubutu. Akwai kuma abin da ya shafi dabarun rubuta gajerun labarai da shirin ‘Zamantakewa’ wanda ke tattaunawa kan al’amuran da suka shafi hulɗa da jama’a a rayuwa ta yau da gobe.

Hassana Ɗanlarabawa marubuciyar littafin ‘Hassana Da Hussaina’, kuma ɗaya daga cikin gwarazan gasar Hikayata ta BBC Hausa na shekarar 2022, kuma jigo a cikin wannan zaure ta bayyana cewa, mafi akasari marubutan da suke ciki, marubuta ne na onlayin waɗanda suka fara rubutu daga baya-baya, a wancan lokacin da suka fara rubutu kansu a duhu yake game da abin da ya shafi adabin Hausa. Suna rubutu ne sama-ta-ka babu sanin ƙa’idojin rubutun ballantana yadda za a tsara shi da kyau. Amma bayan buɗe zauren sai aka samar da zaƙaƙuran marubuta kuma malamai a fagen, suke yin darasi game da rubutu da yadda ake yin shi. Ta haka ne kusan marubuta da dama suka fa’idantu suka gyara rubutunsu har zuwa yanzu suka zama wasu gawurtattu a duniyar marubuta.

Ta cigaba da cewa, zauren ya kawo cigaba ta hanyar shirye-shirye da ake gudanarwa irinsu Baƙon Mako, Saki Ranka, Muhawara, Wasa Ƙwaƙwalwa, Da dai sauran su. Waɗannan shirye-shirye suna da matuƙar fa’ida ga marubuta, ta hanyar sanin junansu, ɓuɓɓugo da ilimi da musayar shi ga juna, warware matsalolin juna ta sigar ilimi da shawarwari.

Har’ilayau, a zauren ne ake gabatar da gasar wata-wata, wadda ta sake ɗaga darajar marubuta da yawa na zauren kasancewar sun samu nasara a gasar.

A cewar, Amrah Auwal Mashi fitacciya a cikin zauren Marubuta, kuma marubuciyar littafin ‘Haƙƙin Uwa’, zauren Marubuta ba a ɓangaren gyara ko kiyaye ƙa’idojin rubutu kawai ya tsaya ba, har ma da ɓangaren da ya shafi rayuwar marubuta ta zamantakewar su da iyali da sauran al’umma. Domin a cewarta, ta dalilin shirin marubuta na samun damar furzar da damuwoyinsu da samun mafita a tsakaninsu. Gyaran zamantakewar aure, da samun damar sanin wasu manyan marubuta da neman shawararsu, ta dalilin zaman tare a cikin zauren.

Fahimtar Gimbiya Amrah ya yi daidai da na Malama Hadiza D. Auta wacce ta kasance babbar yaya a wajen marubuta da dama a cikin zauren. Ita ma tana ganin zauren ya kasance wani dandali na musanyar ilimi da girmama juna a tsakanin tsofaffi da matasan marubuta, da kuma taimakawa juna a tsakanin mambobin zauren, musamman a lokacin da wani ko wata ke shirin aure, ko kuma yayin da wani ko wata ke fuskantar wata jarabawar rayuwa. Hakan ya sa zumuncin da ke tsakanin marubuta ya ƙara ƙarfi sosai.

Malam Abou Outhaymeen shi ma ya jaddada cewa, wannan tallafi da ake haɗawa a tsakanin marubuta yana taimakawa sosai wajen sake ƙarfafa zumunci, da kuma ƙara kusanto da marubuta zuwa ga abin da ya shafi al’amuran addini. Idan za mu iya tunawa a cikin watan azumin Ramadan da ya gabata, Abou Outhaymeen shi ya jagoranci saukar karatun Alƙur’ani da marubutan suka gudanar a wannan zauren.

Kenan za a iya cewa zauren ya zama kamar wata makaranta ce da ake amfana da ilimmai masu yawa, ba kawai ga abin da ya shafi harkar rubutun adabi ba, har ma da ɗaukacin rayuwa bakiɗaya. A cewar Bamai, ko tambaya marubuci ya yi a cikin zauren za ka ga an samu wani masani a fannin ya bashi amsa cikin ilimi da hujja, ba tare da ɓata lokaci ba. 

Gabaki ɗaya marubutan da na samu tattaunawa da su sun yaba ƙwarai da yadda marubuta ke zumunci a tsakaninsu, da girmama na gaba da su, da kuma taimakon da masanan cikinsu ke yi musu na ilimantarwa da horarwa game da hanyoyin inganta rubutu da rayuwa. Gimbiya Amrah Mashi ta ba da shawara ga mambobin cikin zauren marubuta da cewa su ƙara zagewa kan abubuwan da suke yi na alheri. Sannan su ƙara ba da himma wurin kwasar darussan da ake gabatarwa a ciki. Su cigaba da ƙoƙarin zumunci da haɗin kai, su kuma ƙara ƙaimi, su ƙara zama jajirtattu.

Ni ma kuma zan ƙara da nawa shawarwarin kan cewa, nan gaba idan za a yi irin wannan babban taro a riƙa shirya laccoci da faɗakarwa na musamman, kuma a fitar da wani take wanda tattaunawar taron za ta mayar da hankali a kai. Sannan a gayyato malamai daga jami’o’i da jihohi ko ɓangarori daban-daban suna gabatar da maƙaloli, don baƙi da za su zo su tafi da tsarabar ilimi da dama. A riƙa gayyato tsofaffin marubuta daga wasu wurare suna halartar taron da bayar da shawarwari, domin kuwa zauren ya kasance wata duniyar marubuta ce a dunƙule, kada ya zama fuskoki iri ɗaya ne koyaushe ake gani. 

Sannan in da hali nan gaba a riƙa shirya irin wannan taro na shekara-shekara a wasu jihohi ba Kano kaɗai ba, domin bai wa sauran marubuta da ke nesa ba da tasu gidunmawa. Na lura taron bana bai samu cika yadda ake sa rai ba, saboda wasu dalilai masu nasaba da halin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar nan, da kuma yadda mai yiwuwa aka taƙaita gayyatar. 

Allah Ya ƙara haɗa kan marubuta, ya albarkaci rubuce-rubucen su, don cigaba da ilimantar da al’umma.

By ukarofi