
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC), ya ce layukan gidajen mai da al’umma ke fuskanta musamman a jihohin Legas da Abuja na faruwa ne sakamakon sauyin yanayi da ake ciki.
Wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun babban jami’in hulɗa da jama’a na kamfanin, Olufemi Soneye da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, ta ce shiga sauyin yanayi ya haifar da matsalar layin mai domin hakan ya shafi shirya manyan motocin da ke raba man da kuma safararsu wanda hakan ya sa aka samu ragowar samar da isasshen man fetur ga jihohin.
Sanarwar ta ce “saboda yanayin ɗumamar dangogin man fetur da kuma la’akari da dokar hukumar kula da yanayi ta ƙasa (NIMET), ba zai yiwu a shirya man ba saboda tsawa da walƙiya da ake yi a lokacin ruwa sama”.
Saɓa wa dokar NIMET ta hanyar cigaba da samar da man yadda aka saba, zai haifar da haɗari ga motocin, gidajen man da kuma rayukan mutane.
Sannan, an samu ambaliya a hanyoyi da dama da motocin ke bi wajen kai man Abuja daga wuraren da ake ɗakko su.
NNPC ya ce suna cigaba da ƙoƙari wajen ganin an warware matsalolin tare da samar da isasshen man ga yankunan da lamarin ya shafa.
