‘Ƴan bindiga sanye da hijabi sun yi garkuwa da mutane 25 a Katsina

Spread the love

‘Yan bindiga sanye da hijabi wanda aka fi sani da abaya sun sace mutane 26, mafi yawansu mata da yara,a wani hari da suka kai Runka da ke ƙaramar hukumar Safana ta Jihar Katsina.

Al’ummar Runka tana ‘yan kilomita kadan daga dajin Rugu wanda ya dade yana zaman mafakar ‘yan ta’adda.

Wani shaida ya sanar da Channels Television ta waya a ranar Litinin cewa ‘yan bindigar sun kai hari a ranar Asabar da dare a wajen karfe 10:00 na dare. Ya ce ‘yan bindigar suna ta harba wuta a ko’ina a cikin garin.

Ya ce harin ya faru ne sakamakon ayyukan masu bada bayanan sirri na ‘yan bindiga waɗanda mafi yawansu ‘yan garin ne.

“‘Yan bindigar ba su kashe kowa ba a cikin garin sai dai mutum ɗaya da aka harba ya ji rauni bayan ya yi kokarin gudu. Yanzu haka an kai shi asibiti.

“Sun sace mutane 25 ko fiye domin, cikin yanuwana, an sace mutane goma sha biyu.

“Babu wani jami’in tsaro a lokacin harin ke gudana har na tsawon sa’o’i. Bayan faruwar lamarin ne aka aiko da motar sojoji tare da ‘yan sanda don sintiri a yankin.

“‘Yan fashin sun shiga ko’ina a cikin garin. Sun yi ta shiga gida-gida, suna karya kofofin shiga suna kuma ɗaukar mutanen zuwa cikin daji.

“A lokacin harin, an ji ɗaya daga cikin ‘yan fashin yana magana ta waya da wani ɗan leƙen asiri da ba a san shi ba yana gaya masa cewa, ‘Yau, mun zo garin ku’.”

Sai dai har yanzu hukumar yan sandan Jihar Katsina basu tabbatar da wannan labarin ba. Amma shugaban ƙaramar hukumar Safana ya tabbatar da faruwar wannan al’amari.

By ukarofi