‘Yan sanda sun kama wanda ya yi yunƙurin kashe kansa a Abuja saboda tsadar rayuwa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Rundunar ‘Yan sanda a Abuja, ta kama wani mai suna Shuaibu Yusuf sakamakon hawa hasumiyar gidan radiyon Aso da nufin faɗowa ƙasa saboda tsadar rayuwa.

A ranar Litinin ne mutumin wanda ɗan Maiduguri ne a jihar Borno, ya kwashi ƴan kallo a lokacin da ya hawu ƙolin hasumiyar da ke dutsen Katampe inda ya sha alwashin faɗowa ƙasa matuƙar gwamnatin tarayya ta ƙi dawowa da tallafin da ta cire.

Sanadiyar haka, ‘Yan sanda na tsare da shi bayan da ya karɓi rarrashin Darakta Janar ta offishin bada agaji ta gaggawa (FEMD), Florence Dawon Wenegieme inda ta buƙaci ya janye daga mummunan matakin ƙisa kan da ya ɗauka sannan ta bada umarnin a sauke hasumiyar saboda gujewa aukuwar irin haka nan gaba.

A wata takarda da ke ɗauke da rubutun hannu, Yusuf ya zayyano matsaloli tara da ya yi kira ga gwamnati ta magance su ciki har da batun cire tallafin man fetur da kuma rashin tsaro da ake fama da shi a Arewa maso Gabashi da Yammacin Nijeriya.

Sannan, a cikin takardar ya ce zai bada rayuwarsa ne matuƙar za a samu warwarewar matsalolin a sakamakon haka, inda ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su goyi bayan sa a kan haka.

Sai dai, a yayinda kisan kai a Nijeriya ba laifi ba ne, yunƙurin hakan laifi ne kamar yadda dokar laifukan sata na sakin-layi 327 ya nuna inda ta ce za a hora mai irin laifin da hukuncin shekara ɗaya a gidan yari.

By Babaji