Kama sana’a ne mafita ga matasa- Pharm. Gali Sule

Spread the love

An yi kira ga matasa a Jihar Kano, musamman wanda suka kammala makaranta da ba su samu aiki ba, da su rungumi sana’o’i don kaucewa zaman kashe wando.Wannan kiran na zuwa ne daga bakin babban daraktan hukumar samar da magunguna da Kayan asibiti ta Jihar Kano.

Famasist Gali Sule ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a gurin bikin cika shekara 10 da kammala makaranta da ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantun sakandiren kimiyya da fassha ta Jihar Kano (KASSOSA) reshen makarantar kimiyya da ke garin Dawakin Kudu aji na shekarar 2014 (Class 2014) suka shirya a ranar lahadin nan.

Darakta-Janar ɗin ya ce saboda matsin tattalin arziki da ake fama da shi a ƙasar nan, da kuma durƙushewar masana’antu da kamfanoni, wanda hakan ya jawo karuwar rashin aikin yi.”zai fi kyau mu tallafawa matasan mu dan su kama sana’a da zata kara rufawa kansu asiri.”Famasist Gali Sule ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, na iya bakin kokarin ta dan samar wa da jama’a abun yi, ta hanyar ba da jari ga dumbin matasa maza da mata tare da gina guraren koyar da sana’o’i guda 10, haɗi da gyarawa da kuma buɗe waɗanda suka lalace.

Daga nan sai ya kuma yabawa ƙungiyar KASSOSA ƙarƙashi Shugabanta na ƙasa, Alh. Balarabe Nuhu Jallah, bisa koyar da sana’o’i ga ‘yan ƙungiyar da ba su sami aiki ba, da kuma ba su tallafi dan dogaro da kai.

Haka kuma Daraktan-Janar na DMCSA din ya yi kira ga sauran rassan kungiyar tsofaffin ɗaliban da su yi koyi da uwar ƙungiyar ta ƙasa wajen koyawa mambobin su sana’o’i da ba su tallafin jari.

Shugaban ƙungiyar ta KASSOSA aji na 2014, Mal.Abubakar Idris Yarima ya godewa baƙin da suka sami damar halartar taron duk da irin hidindumu da ke gabansu.

By ukarofi