Alhaji Abubakar Alhaji (1937–2026): Dan kishin ƙasa da ya yi wa Nijeriya hidima cikin natsuwa da ƙwarewa 

Spread the love

A makon jiya, Nijeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun jami’an gwamnati da suka yi wa ƙasa hidima cikin gaskiya da riƙon amana, wato Alhaji Abubakar Alhaji (Sardaunan Sakkwato). Rasuwar wannan dattijo ɗan kishin ƙasa, tsohon Ministan Kuɗi, kuma tsohon Jakaden Nijeriya a Birtaniya, bankwana ce da wani mutum wanda rayuwar sa ta kasance abar koyi ta ladabi, kishin ƙasa, tawali’u da sadaukar da kai wajen bautar ƙasa.

Alhaji Abubakar Alhaji ya rasu bayan ya shafe makonni yana fama da rashin lafiya. Da farko an kwantar da shi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo da ke Sakkwato, kafin daga bisani a mayar da shi Asibitin Alliance da ke Abuja, inda Allah ya karɓi ran sa. Mutuwar sa ta zama babban giɓi, domin ta ɗauke ɗaya daga cikin ragowar jami’an gwamnati na wani zamani da suka ɗauki muƙamin gwamnati a matsayin amanar al’umma, ba wata kafa ta tara dukiya ko biyan buƙatun kai ba.

An haifi mariganyin cikin fitacciyar gidan daular sarautar Sakkwato, kuma ya rayu da mutunci da tawali’un da suka dace da irin wannan asali. A matsayin sa na Sardaunan Sakkwato, ya riƙe ɗaya daga cikin manyan sarautun gargajiya mafi daraja a Daular Sakkwato, sarautar da aka fi dangantawa da marigayi Sa Ahmadu Bello, Firimiyan Jihar Arewa. Duk da girman matsayin sa da martabar asalin sa, ya kasance mutum mai sauƙin kai, mai kusantar jama’a, kuma wanda ya samu girmamawa daga mutane ba tare da la’akari da bambancin siyasa, addini ko ƙabila ba.

Tarihin sa a aikin gwamnati abin alfahari ne. Ya fara aikin Gwamnatin Nijeriya a cikin 1964, inda ya riƙa hawa matakai har ya zama Babban Sakatare na Ma’aikatun Kasuwanci da kuma Kuɗi na Tarayya. A wani muhimmin lokaci a tarihin tattalin arzikin Nijeriya, ya taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da bashin ƙasar na waje, sannan ya kasance cikin tawagar da ta tattauna Yarjejeniyar Lome ta Biyu. Waɗannan ayyuka sun buƙaci ƙwarewa ta musamman da hikimar yanke shawara cikin natsuwa—halayen da ya shahara da su.

Naɗin da gwamnatin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi masa a matsayin ƙaramin Ministan Kasafi da Tsare-tsare, sannan daga bisani Ministan Kuɗi, ya nuna irin amincewar da aka yi da ƙwarewar sa. Ya gudanar da waɗannan muƙamai cikin tsantseni da riƙon amana, lamarin da ya sa aka san shi a matsayin ƙwararren mai kula da harkokin kuɗin ƙasa. Daga bisani kuma aka naɗa shi Jakaden Nijeriya a Birtaniya, inda ya sake nuna bajintar sa a fannin diflomasiyya da kare muradun ƙasar nan cikin ƙwarewa da mutunci.

Ko bayan da ya bar muƙaman gwamnati, ritayar sa ba ta yanke hidimtawar da yake wa al’umma ba. Ya ci gaba da ba gwamnatocin jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara shawara a matsayin Mai Ba da Shawara Musamman kan Harkokin Tattalin Arziki. Cikin karamci da kishin ƙasa, ya riƙa amfani da gogewa da ilimin sa ga matasa masu aiki a gwamnati. A wajen sa, bautar ƙasa ba aiki ne na ɗan lokaci ba, illa kira ne da ya kamata a ci gaba da amsawa har ƙarshen rayuwa.

Saƙonnin ta’aziyyar da suka biyo bayan rasuwar sa sun bayyana irin rayuwar da ya yi. Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana shi a matsayin “ginshiƙin aikin gwamnati, gogaggen jami’i kuma ɗan kishin ƙasa,” yana yaba zurfin ilimin sa, riƙon amana wajen kula da kuɗin ƙasa da kuma ƙwarewar sa a harkokin diflomasiyya. Shi ma tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida, ya ce ba kawai fitaccen jami’in gwamnati aka rasa ba, har ma ya rasa “aboki, abokin aiki, amintacce kuma ɗan uwa.” Irin waɗannan kalaman ta’aziyya daga shugabanni da aka yi a zamani daban-daban suna nuna irin daraja da girmamawar da mariganyi Alhaji Abubakar Alhaji ya samu sakamakon shekaru masu yawa na hidima cikin gaskiya da aminci da ya yi.

Babban abin da za a riƙa tunawa da shi ba wai muƙaman da ya riƙe kaɗai ba ne, har ma da kyawawan ɗabi’un da ya rayu da su. Ya fito ne daga wani zamani da ake ɗaukar gaskiya da riƙon amana a matsayin mafi girman cancantar shugabanci. Bai kasance mai neman jayayya ko fitina ba, ya rayu cikin mutunci da natsuwa, kuma ko yaushe ya fifita muradun ƙasa a kan son zuciyar sa. A wannan zamani da amincewar jama’a ga hukumomi take fuskantar ƙalubale, rayuwar sa tana tunatar da mu cewa har yanzu shugabanci nagari da tsare gaskiya yana yiwuwa.

ƙalubalen siyasa da tattalin arziki da Nijeriya take fuskanta a yau sun sa rasuwar sa ta fi zama mai raɗaɗi. A daidai lokacin da ƙasa ke buƙatar dattawa masu hikima, masu tarihin aiki da kuma shugabannin da za su fifita ƙasa a kan kan su, rashin mutane irin Abubakar Alhaji babban rashi ne. Dattawan ƙasa masu irin wannan ƙima ba shawara kaɗai suke bayarwa ba; suna ƙarfafa gwiwar al’umma, suna jagorantar matasa, kuma suna nuna cewa kishin ƙasa yana bayyana ne ta hanyar hidima ta gaskiya.

Yayin da iyalan sa, abokan sa, abokan aikin sa da masoyan sa suke jimamin wannan babban rashi, mu ma muna tare da ‘yan Nijeriya wajen girmama rayuwar da aka sadaukar domin bautar Allah da kuma hidimar ƙasa.

A Manhaja, muna miƙa ta’aziyyar mu ga iyalan sa, Mai Alfarma Sarkin Musulmi da Majalisar Masarautar Sakkwato, gwamnati da al’ummar Jihar Sakkwato, da kuma ɗimbin abokan sa da masu yi masa fatan alheri a faɗin Nijeriya. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa kurakuran sa, ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomar sa, kuma ya bai wa iyalan sa da duk masu ƙaunar sa haƙurin jure wannan babban rashi.

Ko da muryar Alhaji Abubakar Alhaji ta yi shiru har abada, dole ne kyawawan ɗabi’un da ya tsaya a kan su—wato gaskiya, kishin ƙasa, ƙwarewa da hidima ba tare da son kai ba— su ci gaba da zama jagora ga Nijeriya. ƙasar nan tana matuƙar buƙatar ƙarin dattawan ƙasa masu irin halin sa da jajircewar sa, musamman a wannan lokaci mai cike da ƙalubale. Za a ci gaba da tunawa da ayyukan sa, amma hikimar sa, natsuwar sa da nagartaccen shugabancin sa za su kasance abin kewa matuƙa.

By ukarofi

Leave a Reply