
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Majalisar Wakilai ta buƙaci gwamnatin tarayya ta dakatar da batun zartar da yarjejeniyar Samoa har sai abubuwa sun lafa. Majalisar ta yanke hukuncin ne sakamakon kiran gaggawa kan lamarin wanda ya shafi ƙasa da wasu ƴan majalisu 88 suka yi.
A lokacin da yake magana kan batun, ɗan majalisa Aliyu Madaki ya yi ƙarin haske kan sakin layin da ke magana a kan ‘gender equality’, wato ‘a samu daidaiton jinsi’ inda ya ce wannan ka iya cin karo da al’adun ƴan Nijeriya.
Majalisar ta kuma yi kira ga kwamitin da ke da alhakin shiga batun da su gudanar da bincike kan sharuɗan da suka saɓa a cikin batutuwan da yarjejeniyar ta ƙunsa.
An samu saɓanin fahimta kan yarjejeniyar Samoa da gwamnatin tarayya ta sanya wa hannun tare da ƙungiyar Tarayyar Turai wanda da dama daga cikin al’umma suka fahimci hakan a matsayin amince wa auren jinsi ne Nijeriya ta yi.
Sannan, yarjejeniyar Samoa ta haifar da cecekuce a shafukan sada zumunta inda da mutane da dama ke sukan auren jinsi wanda hakan ya saɓa wa dokar hana auren jinsi da aka sanya a kundin shekarar 2014, zamanin shugaba Goodluck Jonathan.
Kazalika, a wata hira da aka yi da ministan kasafi da shirin tattalin arziƙi, Atiku Bagudu tare da takwaransa na yaɗa labarai, Mohammed Idris, sun ce Nijeriya ba za ta saurari duk wata yarjejeniya da ta ci karo da dokokin ƙasa da ma addinai da al’adun al’ummarta ba.
