Gwamnan Jihar Zamfara ya amince da fara ginin sabuwar tashar mota na zamani a cikin Gusau, wanda takai kimanin N4,854,135,954.53. Aikin kwangilar a bada shi ga Fieldmark Construction ltd. Wannan na ɗaya daga cikin ayyukan raya birni wanda gwamnatin sa ke aiwatar wa.
Wannan ya faru ne, a ranar Talata yayin zaman majalisar gudanarwa na gwamnatin, kamar yadda mai magana da yawun Gwamnan,Sulaiman Bala Idris ya shaida.
Yace majalisar ta zanta akan abubuwa da dama wanda suka shafi cigaban mutanen Jihar Zamfara.
Ma’aikatar ayyuka tare da Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi su zasu ɗauki nauyin biyan wannan aiki.
Sabuwar tashar za ta zama ta zamani wadda ta ƙunshi abubuwa na more rayuwa kamar wajen saukar ɓaki, wajen wankin mota, wajen aikin PoS da ofisoshi.
