Majalisa na zargin Ministar Mata da kashe miliyan N75 wajen sayen ƙunzugun mata

Spread the love

Ana zargin ministar harkokin mata ta Tinubu Uju Kennedy, da almundahana kuɗi kimanin naira miliyan 20 wajen sayen ƙunzugu na mata da kuma naira miliyan 45 wajen bikin sabuwar shekara.

Wannan ya fito ne lokacin da aka gayyaceta majalisa domin tuhumar rashin biyan yan kwangila kuɗinsu, kimanin biliyan 1.5 bayan gwamnati ta biya wannan kuɗin.

Amma minstar ta musanta zargin hakan, tace ya faru ne lokacin tsohuwar gwamnati.

Tuhumar ta samo asali ne lokacin da ɗan kwangilar ya shigar da koke gaban majalisa. Akan ayyukan da yayi kuma an kasa biyanshi haƙƙinshi.

By ukarofi