Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Akwai yiwuwar samar da sabuwar jiha nan ba da jimawa ba, sakamakon yadda aka gabatar da ƙudirin kafa jihar Tiga daga Kano a majalisar dattawan Najeriya.
Ƙudurin dokar wanda Sanatan Kano ta kudu Suleiman Abdurrahman Kawu Sumaila ya gabatar, wanda aka yi masa karatu na farko a ranar 10 ga Yuli, 2024.
Ƙudirin doka mai taken “Constitution of the Federal Republic of Nigeria, 1999 (Alteration) Creation of Tiga State Bill, 2024 (SB.523)” na da nufin raba jihar Kano zuwa jihohi biyu, inda Tiga za ta zama sabuwar jihar da za a ƙirƙireta daga Jihar kano .
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Majalisar Dattawa ta karɓi ƙudirin kafa Jihar Anioma a yankin Kudu maso Gabas, wanda Sanata Ned Nwoko daga Delta ta Arewa ya gabatar.
Kazalika, an gabatar da kudirin dokar kafa jihar Orlu, wanda Sanata Osita Izunaso da mai wakiltar Ikenga Ugochineyere, da kuma jihar Etiti suka gabatar, wanda dan majalisa Amobi Godwin Ogah da wasu ‘yan majalisa huɗu daga al’ummomin da abin ya shafa suka dauki nauyinsa.
Sannan akwai kuma kiraye-kirayen a kirkiro sabbin jihohi daga Legas da sauran sassan kasar nan.
