An dakatar da shari’ar tsohon ministan Buhari bayan ya yanke jiki ya faɗi a harabar kotu

Spread the love

An dakatar da shari’ar tsohon ministan wuta, Saleh Mamman a babbar koto dake Abuja saboda bashi da cikakkiyar lafiya.

Tsohon ministan zai gurfana ne yau domin cigaba da shari’ar sa, amma ya yanke jiki ya faɗi. Wanda lauya mai kare shi, ya sanar Alƙalin halin da ake ciki lokacin da aka kira shari’ar.

Tsohon ministan ya bayyana a gaban kotun ne, da kayan sa a jiƙe, wanda ya sanya alƙalin ya tambaye ko ruwa ake a waje.

Mai shari’a Okong,ya tambayi tsohon ministan ko zai iya cigaba da tsayuwa, wanda yace zai iya. Ya faɗi ne saboda maganin da ya sha bai ci abinci ba.

Amma duk da haka, mai shari’a ya ɗage karar sai ƙarfe ɗaya a ka dawo.

Saleh Mamman, ya kasance tsohon minista ne a gwamnatin Buhari. Buhari ya kore shi daga aiki shi da ministan noma bisa zargin almundahana da dukiyar al’umma.

By ukarofi