Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Har yanzu ƙungiyar ƙwadago ta dage kan cewa N250,000 ta kasance mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a Nijeriya, in ji Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago Festus Osifo a ranar Talata.
Osifo ya kuma bayyana cewa TUC da ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya suna ganawa da jami’an gwamnatin tarayya domin cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi.
Ya bayyana hakan ne a babban taron ƙungiyar mata da man fetur da iskar gas a Abuja, mai taken ‘The Dynamic Woman: Naɓigating Challenges in a Constantly Eɓolɓing World’.
Tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikata ya tsaya cik bayan shawarar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yanke na tuntuɓar masu ruwa da tsaki kafin a aika da ƙudirin dokar ga majalisar dokokin ƙasar.
Gwamnatin Tarayya da masu zaman kansu sun amince da Naira 62,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi, amma ma’aikata sun dage a kan Naira 250,000.
Da yake jawabi a wurin taron, Osifo ya ce ba a yi watsi da tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi ba, sai dai ma’aikata da gwamnati sun yi ta gyara lamarin.
“Tattaunawar mafi ƙarancin albashi ba za ta mutu ba. Mafi ƙarancin albashi na 2019 (wanda ya ƙare) ya ɗauki kimanin shekaru biyu don ganin hasken. Mun fara tattaunawar ne a cikin 2017.”
Shugaban na TUC ya ce “Mun yi muku alkawari lokacin da muka fara a watan Janairu (wannan shekarar) cewa za mu tabbatar da cewa wannan yana cikin sauri – an bi diddigin mu don kada mu kasance cikin ruɗani da muke ciki a 2019 wanda ya ɗauki shekaru biyu,” inji Shugaban TUC.
Ya dage cewa ana samun kulawar mafi ƙarancin albashi, inda ya ƙara da cewa shugaban ƙasar na son a ƙara tuntuɓa kafin ya miƙawa majalisar dokokin ƙasar.
“Saboda haka inda muke a yau, mun gabatar da matsayi daban-daban a cikin watan Yuni, lokacin da muka yi hakan, kun san a fili cewa Shugaban Ƙasa ya fito ya ce yana son tuntuɓar hukumar ta gwamnoni, shugabannin ƙananan hukumomi, kamfanoni masu zaman kansu da na ƙwadago, don haka mun ɗauki wani matakin tattaunawa.
“Domin abin da za a miƙa wa Majalisar Dokoki ta ƙasa a zahiri ya zama mafi ƙarancin albashin da za a biya talakawa, don haka a kafafen yaɗa labarai ba ihu muke yi ba, muna yin wani mataki na ayyukan cikin gida, don haka za a gabatar da wannan lissafin da gaske nan ba da jimawa ba. Har yanzu mun nace akan N250,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi,” inji Osifo.
Ba gudu ba ja da baya kan N250,000 mafi ƙarancin albashi – TUC
