Gine-gine da fentin makarantu ba shi ne zai warware matsalar ilimi ba – Farfesa Kamilu Sani

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano


Taron tattaunawa akan makomar ilimi da aka yi a Kano abu ne mai kyau, amma masu aiwatar da manufofi da aka cimma shi ne abin kokwanto, za a kawo takardu da shawarwari a bai wa gwamnati anan siyasa take shigowa inda za a ga any i biris da waɗannan sakamako da aka tsara za a aiwatar.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ɗaya daga cikin mahalarta taron da aka gudanar a Jami’ar Bayero ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a wajen taron.
Ya ce waɗanda alhaki ke kansu na su ga an farfaɗo da ilimi su yi shi da gaskiya ba ya zamanto an siyasatar da shi ba, za a zo a tattauna a gaban mutane kowa ya ɗauki alƙawari da niyyar za a yi a kuma ƙi yin.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ƙara da cewa da za a ce waɗanda ke da alhakin gudanarwa tun daga firamare zuwa jami’o’i su sa ‘ya’yansu a ciki kar ya zamanto ana abin nan da ake cewa a ɗauki maganar Malam amma kar a yi aiki da aikin Malam, abinda yake faruwa kenan, kamata ya yi a zo a yi magana, aikin ma ya tafi yadda ake so.
Ya yi nuni da cewa shekaru 64 da samun ‘yanci kan ƙasar nan, amma an kasa warware matsalar ilimin firamare ma balle sauran matsaloli dalili kuwa shine ba da gaske ake ba, a wajen warware matsalar, idan da da gaske ake ba kawai magana za a yi a ce an ware kuɗi kaza ba, sai gyara abubuwa huɗu na ilimi an bashi muhimmanci.
Ya ce shi ilimi baya samuwa idan babu waɗannan abubuwa ingantattun malamai da manhajar ilimi wacce take ta gaske sannan sai akwai kayan aiki littatafai da dukkan sauran kayan bincike sannan da ɗalibai da kuma makaranta.
Ya ca amma ko da babu makaranta idan dai da waɗannan abubuwa da Kwararrun malamai da manhaja mai kyau da kayan koyarwa za a iya samun ilimi mai inganci.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce saboda siyasar mu domin a gani sai a yi ta gine-gine abar duk waɗancan, baka da malamai waɗanda ma ake da su ba a kula da su an ba su wadataccen albashi da duk abinda zai inganta su ba. Kuma ba manhaja mai kyau sai kawai a yi ta bada muhimanci akan gine-gine da fentin makarantu wanda ba shi ne zai warware matsalar ilimi ba.

By ukarofi