Daga AISHA ASAS
Idan aka ambaci sunan jarumi Kanayo O.Kanayo, abu na farko da zai zowa mai saurare shi ne, tsafi da makamantansu, wanda har a ‘yan baya-bayan nan an samu masu wasannin barkwanci suna amfani da sunansa don isar da saƙo.
Kamar yadda na gani a kwanaki, wani matashi ya yi niyyar yaudarar wata yarinya, har ya fara gaya mata mai zafi, amma tana sanar da shi cewa, Kanayo O. Kanayo ne babanta sai ya fara kuka.
Akwai kuma wani wanda ya je wurin mai nama, ya ce, a yanka masa na kuɗi kaza, bayan ya gama, sai mutumin ya ɗauki waya, ya kira sunan Kanayo O. Kanayo, yana mai sanar da shi ga shi nan ƙarasowa, da wannan ne ya sa mai naman ya ƙi ƙarɓar kuɗin.
Jarumi Kanayo O. Kanayo, ya kasance ƙwararren jarumi da ke shagaltar da masu kallo ta hanyar wasa da ƙwaƙwalwarsu har su kalli fim a matsayin gaske.
Kamar yadda masana harkar finafinai suka faɗa, ba za ka taɓa zama jarumi na gaske ba har sai aktin ɗin ka yi ya yi wasa da zuciyar masu kallo, ta yadda zai sanya su kuka yayin da ka ke ƙoƙarin nuna hakan, ko dariya, ko kuma ban tsoro.
Ƙwararre kuma shahararren jarumi a masana’antar Nollywood, Kanayo O. Kanayo, ya matuƙar kwarewa ne a ɓangaren abinda ya shafi fitowa matsafi da abinda ya dangance shi, asalima fim ɗin tsafi ba ya taɓa cika matuƙar babu jarumin a ciki. Dalilin kenan da ya sa kaso mafi rinjaye na finafinan da ya fito ta wannan ɓangare ne. Wataƙila wannan ne ya sa masu kallo suke ganin kamar a zahiri ma shi ɗin matsafi ne.
Da wannan ne jarumin ya janyo hankalin mutane tare da kawar da tunanin da suke yi kansa, inda ya bayyana a cikin wata tattaunawa cewa, ƙwarewa ce ke sa a yi ma kallon halinka ne ka ke bayyawa a finafinai. Ya kuma kafa hujja da jaruma Patience Ozokwor, wadda mutane da dama ke yi wa kallon muguwa mafaɗaciya.
“Kunga Patience Ozokwor, wadda mutane da dama ke mata kallon muguwa a zahirin rayuwa, saboda kawai rawar da ta ke takawa a finafinai. Magana ta gaakiya tana kishiyar halinta ne a finafinai, kuma hakan ke nunin mutum ƙwararren jarumi ne. A zahiri tana da taushin zuciya, idan ka yi mata tsawa, za ta fara kuka, kamar dai yadda ni nake a finafinai a matsayin matsafi, mutumin da ba na ƙwarai ba, amma hakan kishiyar halayyana ne na zahiri.
Matuƙar za ka iya yin aktin ɗin da za ka sa mutane da yawa amincewa halinka ne na zahiri, to wannan ne zai sa a kira ka da jarumi na musamman kuma ƙwararre,” inji jarumi Kanayo O. Kanayo.
