Dalilai biyar da ke sa sauro cizon wasu fiye da wasu

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Mai karatu barkan mu da sake kasancewa, sannunku da ƙoƙarin karanta jarida mai farin jini Manhaja. 

Uwargida damina ta tsaya, hakan na nufin yawaitar sauro a gidajenmu. Wannan ne ya sa shafin Iyali ya kawo maku darasi na musamman kan sauro da tasirinsa tare da dalilan da ke sa ya fi cizon wasu kan wasu.

Wasu za su yi mamaki cewa, sauro na yi wa mutane mabambantan cizo, saidai idan ku ka bi darasin a sannu za ku fahimci abinda ake nufi.

Mutane da yawa na mamakin yadda sauro ke baibaye wasu, yayin da a gefe ɗaya ya yi wa wasu afuwa. Abinda ke ba su mamakk kuwa ganin cewa a gida ɗaya suke, ko ince tazarar da ke tsakaninsu a kwanciya ba mai tsayi ba ce sosai. 

Kafin komai, za mu fara da bayani kan illar sauro ga lafiyarmu. Da yawa sun sani, sakamakon hana barci, boren cizo, ja ga fata sakamakon sosa wurin, saidai kaɗan ne suka san sauro na yaɗa cututtuka masu haɗari.

Kamar yadda rahoton cutar zazzaɓin cizon sauro na duniya na 2022 ya tabbatar, Najeriya ce ta fi kowacce ƙasa yawan masu fama da zazzaɓin cizon sauro a duniya da kashi 27% na masu kamuwa da cutar zazzaɓin cizon sauro.

Baya ga haka, kashi 31% da ke cikin adadin suna mutuwa ne ta sanadiyyar. A ɓangare ɗaya kuwa, Najeriya ta ɗauki kashi 55% na masu fama da cutar zazzaɓin cizon sauro a Afirka ta Yamma a shekarar 2022. Abin tambaya a nan shi ne, me ke sa sauro yi maka soyayyar da ba ya yi wa sauran mutane?

1. Girman Jiki da Nauyin Numfashi:

Sauro na farauta ne ta hanyar amfani da ƙamshi, musamman iskan da muke fitarwa yayin numfashi, wato carbon dioɗide (CO2) a turance. 

Masu manyan jiki daga mutane kuwa suna fitar da iskan na CO2 da yawa, wanda hakan ke sa su zama abin sha’awa ga sauro. 

Maza da mata masu juna biyu, da waɗanda suka manyanta sun fi samun yawaitar cizon sauro ta dalilin nauyin numfashin da suke fitarwa.

Dakta Robert Jones, daga Makarantar Kiwon Lafiya da Magunguna ta London, ya bayyana cewa, ƙiba na ɗaya daga cikin ababen da ke taka rawa a jawo hankalin sauro ga jikin mutum, haka kuma yawan adadin numfashi, kamar lokacin motsa jiki, da kuma numfashi mai nauyi yayin barci na jawo sauro.

2. Ƙamshin Halitta da Kwayoyin Cuta na Fata:

Kamshinmu na musamman, wanda ƙwayoyin halitta da fata microbiota suka rinjaya, shi ma yana gayyatar sauro. Binciken da aka yi inda mutane suka sanya leda don tattara ƙamshinsu ya nuna cewa, sauro na da fifiko ga wasu ƙamshi. 

Abubuwan kwayoyin halitta na iya yin lissafin kusan kashi 67% na sha’awar sauro, saidai har zuwa yanzu masana kimiyya na kan bincike ne kan abubuwan da ke jawo sauro da yadda ake rufe su ko rage su.

3. Launin Kaya:

Ɗaya daga cikin ababen da ke kan gaba wurin jawo ra’ayin sauro shi ne, launin tufafinku. Sauro sun fi son jar kala, ‘orange’ baƙi, da cyan, yayin da kore, shuɗi, bula ke da ƙarancin farin jini ga sauro. Don haka gujewa launuka masu jan hankalin sauro na iya rage yawaitar cizon sauro.

4. Nau’in Jini:

Akwai bayanai da suke cewa nau’in jini, musamman nau’in O, na daga cikin ababen da sauro ya fi yawan bibiya. Duk cewa, wannan nazarin bai kammalu ba, yayin da yake shan raddi daga ɓangarori na ilimi da dama, kamar Dakta Jones wanda ya nuna cewa, nau’in jini ba shi da muhimmanci idan aka kwatanta da sauran abubuwa.

5. Abincin da muke ci da sha:

An tabbar da wasu abinci da abubuwan sha na jan hankali ko korar sauro. Ɗaya daga cikinsu akwai tafarnuwa wadda ke rufe ƙamshin mutum, kuma sauro ba ya son ƙamshin, don haka bai cika kusantar mai ƙamshin tafarnuwa ba, yayin da abinci mai gishiri ko zaƙi ke iya ƙara sha’awar bibiyar mai shi daga sauro. Ita ma barasa kan iya jawo hankalin sauro, kamar yadda ƙaramin bincike ya nuna. 

Dokta Jones ya ba da shawarar yin amfani da abubuwan da aka tabbatar a kimiyyance maimakon dogaro da canje-canjen abinci.

By ukarofi