
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati, EFCC ta gayyaci Shugaban hukumar jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Malam Jalal Arabi zuwa ofishinta da ke Jabi a Abuja.
Rahoto daga ‘News Point Nigeria’ ya ce, EFCC ta gayyaci Arabi ne domin yin bayani game da yadda ya sarrafa Naira biliyan 90 da gwamnati ta bayar na tallafi ga Alhazan Hajjijn 2024.
Haka kuma EFCC za ta gabatar da tuhume-tuhume kan Arabi da NAHCON ciki har da zargin rashin karrama Alhazan yadda ya dace a ƙasar Saudiyya yayin aikin hajjin.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya ce zai yi bincike game da gayyatar tare bayar da cikakken bayani ga manema labaru.
Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan da Arabi ya bayyana wa manema labarai cewa sun bai wa kowane mahajjaci tallafi cikin kuɗin da Gwamnatin Tarayya ta ware mu su, inda kowa ya samu gudunmawar miliyan N1.6 sakamakon rugujewar darajar Naira.
