‘Yan bindiga sun kashe mutum huɗu a Imo

Spread the love

A ranar Litinin ne ‘yan bindiga suka yi wa ‘yan sanda huɗu kwanton ɓauna a unguwar Irete da ke kan titin Onitsha a Owerri, babban birnin Jihar Imo.

A cewar majiyoyi, ‘yan bindigar sun kai farmaki kan ‘yan sandan da ke sintiri a lokacin

An kuma bayar da rahoton kashe wani mai sana’ar PoS da wani mai wucewa a harin da ‘yan bindigar suka kai wa ƴan sandan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Henry Okoye ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce an kashe ‘yan sanda huɗu ba shida ba.

Wannan harin dai shi ne na baya bayan nan a hare-haren da wasu ‘yan bindigar jihar ke kaiwa jami’an tsaro a jihar Imo da shiyyar Kudu-maso-gabas da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da dama a ‘yan shekarun nan.

By ukarofi