Zanga-zanga: Jami’ar Bayero ta ce za ta cigaba da aiki yadda aka saba

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Yayin da kwanakin zanga-zangar tsadar rayuwa ke ƙara kusantowa a Nijeriya, Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Bayero ta Kano, ta ce za a cigaba da gudanar da harkokin makarantar kamar yadda aka saba.

Mataimakin shugaban reshen kula da harkokin al’umma na jami’ar, Lamara Garba ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannunsa inda ya bayyana cewa su na sane da batut fara zanga-zangar a ranar 1 ga watan Agusta.

Hukumar gudanarwar ta sanar da al’umma cewa, za a cigaba da harkoki a jami’ar kamar yadda aka saba, ya na mai shawartar ma’aikata da ɗalibai su cigaba da zama cikin lumana tare da kiyaye doka da oda.

Ya kuma ce a yayin da dokar ƙasa ta bayar da damar zanga-zangar lumana, Jami’ar ta na mai damuwa da zaman lafiyar ma’aikanta da ɗalibanta gami da sauran ababan da makarantar da ta mallaka.

By Babaji