Mahajjatan Nijeriya 30 ne su ka rasu a 2024 – NAHCON

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Hukumar jigilar Alhazan Nijeriya, NAHCON ta ce aƙalla mutane 30 ne su ka rasa rayukansu a yayin aikin hajjin bana.

Shugaban hukumar, Malam Jalal Arabi ya faɗi haka a yayin ganawa da ƴan jarida inda ya ce mutane huɗu ne su ka mutu sakamakon zafin rana da ya haifar da ɗumamar yanayi.

Ya ce, duk da a cewa an sanar da su batun sauyin yanayin, zafin rana a shekarar 2024 ya zama daban saboda tsananinsa.

Ganin haka ya sa hukumar ta samar da kayayyakin kariya da su ka haɗa da lemomi da wasu ababan garkuwa daga shiga matsi a lokacin aikin Hajjin.

Arabi ya kuma ce, Shugaba Tinubu ya ware Naira biliyan 90 don tallafa wa mahajjatan kan tashin gwaoron zabi da farashin zuwa aikin Hajjijn ya yi a bana.

Kazalika, NAHCON ta fitar da tsarin yadda dukkan mahajjatan su ka ci moriyar tallafin inda kowannensu ya samu ragin sama da Naira miliyan 1.6 cikin asalin kuɗin na miliyan 8.45.

Bugu da ƙari, Arabi ya bada tabbacin inganta lamarin tallafin ta yadda mahajjata a nan gaba za su ci moriyarsa a Nijeriya.

By Babaji