Tun ina ƙarama ina karambanin gyaran soket ɗin wutar lantarki da sauransu – Injiniya Amina Muhammad 

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Gimbiyarmu ta wannan mako, wata baiwar Allah ce wacce jajircewa da aiki tuƙuru suka sa ta yi zarra, kuma ta zama abin kwatance a tsakanin mata ‘yan’uwanta. Injiniya Amina Muhammad mace ce mai kamar maza, ta ciri tuta a inda ta kasance ɗaya daga cikin mata ƙalilan da suka karanci aikin injiniyancin lantarki, kuma suke aiki a tsakanin maza. Injiniya Hajiya, kamar yadda ake yi mata laƙabi, ta kasance ɗaya daga cikin injiniyoyi mata da ke aiki a tashar talabijin ta NTA. A zantawarta da Abba Abubakar Yakubu, ta shaida masa burinta na kaiwa ƙololuwar aikin injiniyanci ta hanyar karatu da bincike. 

MANHAJA: Ina son ki gabatar mana da kanki.

INJINIYA AMINA: Sunana Amina Muhammad Umar. Ni ‘yar asalin Jihar Nasarawa ce daga Ƙaramar Hukumar Toto. Amma an haife ni a Jos ne, kuma a nan na yi dukkan rayuwata, har na yi aure. Sannan ni ƙwararriyar Injiniyar lantarki ce, ma’aikaciya a tashar talabijin ta ƙasa (NTA). Ina kuma taɓa kasuwanci. Ina da yara biyu, Maimuna Usman da Muhammad Tahir Usman. 

Ko za ki gaya mana tarihin rayuwarki?

An haife ni a ranar 21 ga watan Disamba na shekarar 1984 a garin Jos na Jihar Filato. Sunan mahaifina Injiniya Muhammad Umar Sa’eed, sunan mahaifiyata kuma Hajiya Maryam Musa (Allah ya jiƙanta da rahaman, Amin). Mu 6 ne iyayenmu suka haifa, mata 5 da namiji ɗaya, kuma nice ‘yar su ta fari. Na yi karatuna na firamare a Rantya Model School, na kammala a 1994. Sai kuma na shiga ƙaramar sakandire a GSS Kufang a ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu. Bayan na yi shekara uku, sai na ci gaba a makarantar Abbah Memorial College Jos shi ma na shekara uku ne sannan na kammala a 2001. Da ga nan na tafi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya dake Bauchi, inda na samu shaidar ƙaramar Diploma da Babbar Diploma a ɓangaren Injiniyancin Lantarki wato Electrical Electronic Engineering. Sannan na yi aikin hidimar ƙasa a Jihar Kaduna a Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na TCN (Transmission Company of Nigeria) da ke Mando a Jihar Kaduna daga shekarar 2011 zuwa 2012. Bayan na kammala hidimar ƙasa sai aka min aure a ranar 7 watan Yuli na shekarar 2012. Na auri tsohon jami’in Hukumar Kare Aukuwar Haɗurra ta ƙasa (FRSC) Arch. Usman Aliyu. Allah ya albarkaci auren mu da yara biyu mace da na miji, Maimuna Usman Aliyu Da Muhammad Tahir Usman, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a ranar 24 ga watan Yuli 2020, (Allah Ya jiƙansa da rahaman, Amin). Na fara aiki a Babbar Tashar Talabijin ta ƙasa ta NTA Lafia a sashin injiniyanci a 2013, inda na kasance Injiniya mace ta farko da ta yi aiki a tashar NTA Lafia, kafin daga bisani na koma NTA Channel 5 a Abuja, sai kuma aka sake yi min canjin wajen aiki na koma Cibiyar Watsa Shirye-shirye ta NTA Network Centre da ke Jos, kuma har yanzu a nan nake aiki. Na koma ƙara karatu a makarantar Defence Academic Postgraduate Schools a Bauchi inda na yi Diploma ta gaba da digiri wato PGD a ɓangaren Injiniyancin lantarki. Yanzu haka ni mamba ce a ƙungiyar ƙwararrun injiniyoyi ta COREN.

Ko za ki kwatanta mana irin iyalin da ki ka fito da yadda tarbiyyar ku ta kasance lokacin tasowarki?

Na rayu ce a cikin wani iyali na ma’aikata kuma masu tsauri a kan tarbiyya. Mahaifiyata malamar makaranta ce, babana Injiniya ne. Na taso cikin kyakkyawar tarbiyya da kula da addini. Mahaifanmu sun ɗora mu ni da sauran ‘yan’uwana mu 6 akan turba ta tsoron Allah da mutunta ɗan’adam. Mahaifiyata (Hajiya Maryam Musa) Allah ya jiƙanta da rahama, ta kasance mai tsauri sosai wajen ladabtarwa da sa ido kan halayyar ‘ya’yanta, musamman kasancewar akasarinmu mata ne. Rayuwarmu ta kasance cikin wani irin tsari akwai lokacin karatu, akwai lokacin wasa, da na ayyukan gida, muna kuma zuwa Islamiyya bayan mun taso daga boko, wannan kam babu fashi.

Wanne abu ne ya ja hankalinki ki ka zaɓi ki karanta ɓangaren kimiyya, musamman ma sashin injiniyanci?

To, da farko dai aikin likitancin masu kula da lafiyar ƙananan yara naso na koya a jami’a, amma Allah bai yi ba. Don ban samu damar shiga jami’a ba a lokacin da na nemi shiga Jami’ar Jos. Daga baya ne na nemi shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Federal Polytechnic Bauchi, in da na nemi damar yin karatu a sashin injiniyancin lantarki, kuma na yi sa’a suka bani. Duk da dai na yi wa karatun injiniyanci kallon aikin maza, don na taso ina ganin babana yana aikin injiniyanci. Sai nake tunanin aikin injiniyanci aikin maza ne kaɗai. Mahaifiyata ce ta bani ƙwarin gwiwa kan cewa tasan zan iya, don su ma mazan da suke yi ba kai biyu ne da su ba. Kuma ina ganin aikin injiniyanci ƙaddarata ce, Allah ne Ya san hikimar hakan, domin tun ina ƙarama ina karambanin gyaran soket ɗin wutar lantarki da sauran abubuwan lantarki na gida.

Ana yi wa ilimin kimiyya da fasaha kallon wani ɓangare mai wahalar karatu, yaya ki ka ji lokacin kina makaranta kuna karatu tare da maza?

E, gaskiya ne. Karatun injiniyanci akwai wahala sosai. Sai mutum ya kasance jajirtacce kuma mai son karatu, mai azama, mai haƙuri, mai juriya. Lokacin da nake karatu na mayar da hankali na akan karatuna, kuma malamanmu da ɗalibanmu sun ba ni haɗin kai sosai, in ban gane abu ba ina samun su su koya min. Gaskiya duk da dai da son samu ne a ce akwai ɗalibai mata da yawa, amma mazan da muka yi karatu da su sun ɗauke ni kamar ‘yar’uwarsu, ban ji wani kaɗaici ba.

A lokacin da ku ke karatu mata ku nawa ne a ajin ku, kuma kina ganin ana bai wa mata dama iri ɗaya da maza su yi karatun da suke so?

A lokacin da muke makaranta, mata mu 5 ne kaɗai a ajinmu. Kodayake yanzu ana samun cigaba sosai, amma har yanzu akwai iyayen da wani sashi na al’umma da suke ganin akwai karatun da bai kamata mata su yi ba.

Kin taɓa yin takaici ko nadamar wannan ɓangaren aiki da ki ka zaɓa, a makaranta ko a wajen aiki?

Gaskiya akwai lokacin da na yi takaicin zaɓin karatun injiniyanci da na yi, a lokacin muna shekarar ƙarshe a makaranta, saboda tsananin da karatun da muke yi. A lokacin muna tare da ƙanwata a ɗaki ɗaya, ita tana karanta harkokin kasuwanci, amma ba na haɗuwa ta ita don kafin ta tashi na tafi aji kuma kafin na dawo ta yi barci. A lokaci ita ce ta yi ta ban baki, tana ƙara min ƙwarin gwiwa, tana cewa ai dama idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi. Kuma tun lokacin ban ƙara yin nadamar karantun injiniyanci ba. Don sau da yawa akwai wasu mata da maza dake cewa na zama abin koyi a wajensu. Kuma hakan na sa ina jin daɗi a raina, ina ƙara ganin kimar karatun da na yi.

Yanzu da ki ke aiki tare da maza bayan kammala karatunki, shin kina samun ƙwarin gwiwa a aikin da kike yi?

Alhamdulillah, suna bani ƙwarin gwiwa da goyon baya sosai.

Ba sa tauye min haƙƙina, suna kuma taimaka min a kodayaushe, don ganin ban samu wata matsala ba a wajen gudanar da aikina.

Shin tun da farko karatun da ki ka yi na aikin injiniyanci zaɓinki ne ko don mahaifinku ma aikin da yake yi kenan?

Aiki injiniyanci zaɓina ne, kuma zaɓin Allah ne. Don na tabbata koda mahifinmu ba ya aikin injiniyanci, iyayena za su bani goyan baya akan abin da nake so in yi, matuƙar bai saɓa wa addini ba. 

Shin za ki goyi bayan ‘yarki ta koyi aikin injiniyanci?

E, ƙwarai ma kuwa. In dai tana so zan goya mata baya ɗari bisa ɗari. 

Waɗanne kalmomin ƙarfafa gwiwa za ki bai wa duk wata yarinya da ke sha’awar karatun injiniyanci?

Ina so su sani cewa injiniyanci ba aikin maza ba ne kawai, mace ma tana iya yi har fiye da mazan. Kuma ta kasance tana mayar da hankali sosai akan karatunta. In dai ta yarda da haka to, za ta iya, kuma babu abin da zai gagareta. ln sha Allahu za ta zama duk abin da take so ta zama.

Shin akwai wani abu a aikin injiniyanci da ki ke ganin bai dace a ce mace tana yi ba?

In ma dai akwai bai wuce aikin dare ba, musamman a irin aikin da muke yi na talabijin da muke yi, inda ake aiki tsawon awa 24, ba dare ba rana. 

Wanne abu ne ya fi birge ki da aikin da ki ke yi?

A ce an samu matsala a wani abu, kuma na je na warware ta, ina jin daɗin hakan sosai. 

Idan ba kya aiki wanne abu ki ke yi wanda yake ɗebe miki kewa?

 Ina sha’awar zama a lambu, yana ɗebe min kewa sosai. 

Wanne buri ki ke so ki cimma nan gaba a rayuwarki?

Ina son in ƙara ɗora karatuna har na kai ƙololuwar aikina na injiniyancin lantarki, in Allah Ya yarda. 

Wanne irin littafi ki ka fi son karantawa?

Ina son karatun Alƙur’ani mai girma, da sauran littattafan addini. Sai kuma littattafan da suka shafi tsirrai da furanni. 

Akwai wata mace da ki ke kallo a matsayin madubin rayuwarki, wacce ki ke burin a ce kin zama kamar ita?

Mahaifiyata ita ce allon kwaikwayona! Babu wata mace da nake kallo da daraja da kima fiye wacce ta haifeni. 

Yaya ki ke haɗa aikin ki da kula da iyalinki?

Abu ne da ke buƙatar tsari. Mijina, da Allah ya yi wa rasuwa, ya kasance mutum mai sauƙin kai da fahimta. Yana taimaka min ƙwarai da gaske, tare da shi muke tsara yadda muke tafiyar da iyalinmu. Allah ya ƙara haskaka makwancinsa. 

Yaya rayuwa ta kasance miki bayan rasuwar maigidanki?

Gaskiya na shiga tsananin ƙunci da firgici sosai, fiye da duk wani abu da ya same ni a rayuwata, bayan rasuwar mahaifiyata. Na yi rashin masoyi, amini, mai jinƙaina da tausayina. Babu shakka rayuwata ta yi matuƙar sauyawa sosai, sai dai kasancewar ina tare da ‘ƴan’uwa, da surukai, da ƙawaye waɗanda suka riƙa ƙarfafa min gwiwa da rarrashina, ya sa na samu sanyi da dangana a raina. A matsayina na musulma na yi imani duk mai rai mamaci ne, kuma kowa yana da wa’adin da Allah Ta’ala Ya ɗibar masa zai yi a duniya. Sai dai mu ce, Allah Ya sa mu cika da imani. Alhamdulillah, yanzu ba na jin wani ƙunci a raina. 

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarki?

In da rai da rabo!

By ukarofi