MAKAMASHI: Mata masu hannaye ba a ɗaura mu su zani

Spread the love

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

Masu karin magana na cewa, “mata masu hannaye, ba a ɗaura mu su zani.” Ma’ana; hannaye da su ake haifuwar kowanne ɗan adam namiji ko mace, kuma da hannaye ake dukkan wasu al’amura na rayuwa. Rashin hannu yana tauye al’amura masu tarin yawa ga rayuwar bil adama, saboda haka duk wata tawaya da ɗan adam ya ke samu walau ta ido ko kunne ko kuma ƙafofi, idan mutum ya na da lafiyayyun hannaye sauran sun zama nafila. Shi ya sa ma aka zo da wannan karin magana, matar da ba ta da hannaye ba ta da wani sirri ga mutuncinta domin kuwa komai na ta na sirri ya zama a bankaɗe.

Wannan ta sa Allah maɗaukakin sarki ya albarkaci duk wata ƙasa ta duniya da wata madafa ta guraren noma da za su noma wata cimaka domin su rayu, haka ya ba su wani makamashi, walau, hasken rana ko iska mai ƙarfin gaske ko ruwa mai gudana ta koguna ko rafuka ko kuma gulabe. Haka kuma ya ba su ma’adanai launi-launi domin su sarrafa su zuwa wasu abubuwa da za su sauƙaƙa kuma su tallafawa rayuwarsu. Misali; a Najeriya an ba mu filayen noma da kiwo, mu ne na farko a duk faɗin Afrika ta yamma. Da mun mayar da hankali da Najeriya za ta ciyar da bayin Allah sama da biliyan guda.

Allah ya ba mu hannaye biyu – noma da kiwo, amma saboda rashin ta ido daga talakawa da shugabanni, mutuncinmu ya zube a idan duniya saboda fatara da yunwa da kuma karatun jahilci mun zama mabarata Allah ya ba ku mu samu. Sai masifu suka kunno kai tun daga 1967, lokacin mulkin Yakubu Gowon, har yanzu a na hasashen cewa, nan da shekara ta 2030 ’yan Nijeriya sama da miliyan 80 za su faɗa rijiya gaba dubu ta yunwa, idan hukumomi ba su yi wani abu na haƙiƙa ba. Bari mu yi matashiya da Maguzawan zamani da suke cewa, “yunwa ba a yi ma ta lahaula, sai ɗan ƙanzo.”

Allah ya rufa wa ƙasar nan asiri da ba ta hannaye guda biyu masu tasirin gaske makamashi da ma’adanai sama da hamsin, wanda duniya ta ke buƙata da zai taimaki al’ummar duniya sama da biliyan takwas. Kwal, man fetur, gas da kuma makamashin yureniyum (Uranium) banda rana da take buɗewa sama awa 12, ga kuma Kogin Kwara da na Binuwai, amma saboda rashin godiyar Allah yau shekaru 64 an kasa ba wa ’yan Najeriya kashi 40 na hasken wutar lantarki na tsahon awa 12 kacal.

Bari mu sauya, mu je ga ma’adanai ƙididdiga ga ta nuna cewa babu jahar da ba ta da ɗaya zuwa uku na ma’adanai da duniya ta ke buƙata, bari mu ɗauki jihata ta Kano, mu ɗauki ma’adanai guda uku – taɓo na ginin tukwane (ceramic) da yashi na samar da gilashi da ƙarau (glass), marmara ta yin tayils na adon ɗakuna da guraren taron jama’a da kuma banɗakuna, wato makewayi. Waɗannan masana’antu za su samar da aikin yi ga dubban matasa, kuma zai samar da kuɗin shiga ga hukuma wanda zai taimaka wajen gina wannan jaha ta Kano.

Idan muka ɗauki, Arewacin Najeriya wato jahohi goma 19, Allah ya ba wannan yanki da ma’adanai kamar gorar ruwa barite, bantonait, barina, tabo (clay), kwal a jahohin Nasarawa da Binuwai da kwalanbit a Jihar Kano da Filato da Katsina da kuma Zamfara. Idan muka tsaya a ma’adinin zinare (gold), jihohin da Kaduna da Zamfara da Sokoto da Neja da kuma Kebbi su kaɗai za su maye gurbin da ake samu daga makamashin man fetur. Idan aka shiga fito da wannan ma’adani zuwa kasuwannin duniya, Najeriya za ta shugaban Afrika ta Kudu a fagen wannan kasuwa.

‘Iron’ bakin ƙarfe da ke Ajeokuta a Jihar Kogi shi kaɗai zai riƙe Najeriya ta zama a gaba a fannin kere-kere a motocin hawa da ma’aikatun gine-gine na hanyoyi da na gidaje da ofishin da filayen wasa da suke neman rodi duka wajen haƙar bakin ƙarfe zai biya wannan buƙatar. Wannan gata da Allah ya yi ma na tun daga mulkin Alhaji Shehu Aliyu Shagari, wanda ya samar da wannan masana’anta ta ƙarafa da ke Ajekouta da wajan mulmula ƙarafa misali na Katsina.

Amma ƙasashen da su ke da’awar dimukraɗiyya Ƙasar Birtaniya da Amurka da Rasha sun hana wannan buri ya tabbata tun daga 1979 zuwa yau. Murtala/Obasanjo sun taka tasu rawa, amma Ajakuta ba ta tabbata ba, haka Buhari yana soja da yana farar hula Ajakuta shiru ka ke ji. Marodona, wato Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi duk hikimominsa na ƙyanƙyasar fasahohi (incubating centres) da guraren kwaikwayar fasahohi, amma Birtaniya da Amurka da Rasha har ma da Faransa da kuma Jamus sukayi kutun-kutun kada Ajakura ta tabbata.

Wannan hassada da kushe da kuma bakin ciki muraran, ba’a so mu amsa kirarin da duniya ke yi mana tun kafin samun ‘yan cin kai na jeka nayi ka da ƙasar Ingila, wato Birtaniya ta ba mu a shekarar 1960. To, Alhamdulillah! Najeriya ta karɓi mulkin dimukraɗiyya tun a shekarar 1999, kuma an ci sa’a Shugaba Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shatima Mustapha, mutane da suke da alƙibla ɗaya, dukkan sun shugabanci jihohinsu a matsayin gwamnoni, haka sun je majalisar taraiya, kujerar sanatoci.

Baya ga haka suna addini ɗaya Islam da ya horar da rashin tsoran duk wani mahaluki, wato babu wani abin tsoro baya ga mahalicci – Allah Subhanahu Wata’ala. Tun da suka iya cire ‘petroleum subsidy’, wato tallafin man fetur. Wannan babbar illa ya yi wa ‘Amurka da ƙasashen yammacin Turai waɗanda su suke more wannan tallafin. Wannan ya fi korar kare da janar Murtala ya yi wa BP wanda ya mayar da shi AP. Haka ya fi tsarin da IBB ya zo da shin a ‘petroleum independent marketers’ da ’yan Najeriya suke lasar wannan garaɓasa.

Waɗancan kamfanoni da suke sharɓar wannan lagwada sama da shekaru 50 su suke kunno wuta ta hanyoyi daban-daban, hauhawar farashi na kayan masarufi babu gaira babu dalili. Fito da ’yan fashin daji da garkuwa da mutane sai an biya kuɗin fansa da masu tayar da ƙayar baya da sunan addini da kuma ɓarayin biro. Da masu kururuwar a buɗe boda da kuma a dawo da tallafi. Wanda Mai Girma Shugaban Ƙasa ya ke cewa, “no going back” hakan ta kai shi da ƙwatowa ƙananan hukumomi 774 hakkinsu daga gwamnoni mahandama da babakere ta kwasar kuɗaɗensu da sunan za a ƙawata biranan su ta yi musu gadar sama ko kuma gadar ƙasa ta hannun ’yan kwangila na ƙasashen waje domin a ji dadin fita da kuɗaɗen. Ko kuma dabarar za a kai matasa ƙaro karatu domin samun digiri na biyu ko na uku. Da yi musu haɗa ba ka da su dawo gida domin su taimakawa ’yan uwansu.

Bari mu ƙarƙare a wannan satin da yin kira ga shugabanni da talakawan su da su ji tsoron Allah da su dawo kan hanya ta yin godiya gare shi da ya ba mu hannaye bibiyu domin rufa wa kanmu asiri ta suturta al’aurarmu – game da fatara da yunwa da kuma hauhawar farashi na kayan masarufi na yau da kullum.

By ukarofi